| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Mutum fiye da 30 sun rasu sakamakon hatsarin mota a Jihar Kano
Gwamnan ya ba da umarnin cewa a yi wa duk waɗanda suka ji rauni a hatsarin magani kyauta a asibitin gwamnati
Mutum fiye da 30 sun rasu sakamakon hatsarin mota a Jihar Kano
Gwamna Abba ya "umarci ma’aikatar kiwon lafiya ta bayar da magani kyauta ga waɗanda lamarin ya rutsa da su”. / Others
9 Fabrairu 2026

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana jimaminsa game da rasuwar fiye da mutum 30 a wani hatsarin mota da aka yi a Kwanar Barde a ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Lahadi ta ambato gwamnan yana bayyana lamarin a matsayin babban rashi ba ga iyalan mamatan kawai ba har ga ɗaukacin jihar.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon tuƙin ganganci da direban wata tirela da ke kan hanyar Gujungu yake yi, “lamarin da ya kai ga mutuwar fiye da mutum 30, yayin da mutane da dama suka jikkata,” in ji sanarwar.

“Gwamnan ya umarci ma’aikatar kiwon lafiyar jihar ta tabbatar da cewa dukkan waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke asibitoci su sun samu magani kyauta ba tare da ɓata lokaci ba,” in ji sanarwar.

Masu AlakaTRT Afrika - 'Yansandan Nijeriya sun fara bincike kan kashe wata mata da 'ya'yanta shida a Kano

“Kana ya ba da umarnin cewa ofishin mai ba da shawara na musamman game da harkar jinƙai a jihar ya yi nazari game da waɗanda lamarin ya shafa ya kuma tsara matakan tallafa wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su,” in ji ta.

Kazalika sanarwa ta ce gwamnan ya bai wa masu tuƙin motoci, musamman masu tuƙin manyan motoci, su ƙaurace wa tuƙin ganganci su kuma bi dokokin tuƙi domin kauce wa irin wannan bala’in nan gaba.