Abubuwan da ya kamata mu sani game da daftarin yarjejeniyar Amurka da Iran

Wannan lamari ba abu ne karami ga Iran ba, wadda ita ma ta sha alwashin kai hare-haren ramuwar gayya kan Amurka sa cibiyoyin makamashi a kasashen Gulf da ke dauke da sansanonin soji da kadarorin kudi na Amurka.

By
Abubuwan da ya kamata mu sani game da daftarin yarjejeniyar Amurka da Iran / Reuters

Tehran da Washington na nazari kan daftarin tsagaita wuta, wanda masu shiga tsakani ke taimaka wa don tabbatar shi, a yayin da wa’adin da Trump ya bayar ke gaf da karewa.

Duniya na kan wani tsini, masu shiga tsakani na yin hanzarin ganin an cim ma yarjejeniyar a yayin da wa’adin daukar mummunan nataki da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar ke karatowa, inda ya ce ko dai Iran ta bude mashigar teku ta Hormuz ko kuma ya yi ruwan bama-bamai kan gine-ginen fararen hula a Iran.

Wannan lamari ba abu ne karami ga Iran ba, wadda ita ma ta sha alwashin kai hare-haren ramuwar gayya kan Amurka sa cibiyoyin makamashi a kasashen Gulf da ke dauke da sansanonin soji da kadarorin kudi na Amurka.

A ‘yan makonnin da suka gabata Trump ya bayar da gargadi sosai, amma barazanarsa ta baya-bayan nan, a ranar Lahadi ta zama mafi kawo kalubale.

Da yake aike wa da sako ta shafin Truth Social, Trump ya yi amfani da mummunan kalami, yana fada wa shugabannin Iran cewa za su rayu a wuta, idan har ba su bude Mashigar Hormuz ba, yana cewa “Talata za ta zama Ranar Samar da Makamashi, Ranar Matsawa Gaba, duk a hade waje daya.”

Hare-Haren Amurka-Isra’ila kan Iran sun yi asarar kusan rayuka 2,000, cikin har da yara kanana, inda wasu dubunnai suka jikkata.

Kasashen yankin da suka hada da Turkiyya. Pakistan da Masar na ta kokarin  shiga tsakani don cim ma tsagaita wuta.

Ga abubuwan da ya kamata ku sani game da  daftarin tsagaita wutar.

Tsagaita wuta mai iyaka

Pakistan ta bayar da shawara da wani tsari mai matakai guda biyu don kawo karshen yakin Amurka-Isra’ila da Iran, wanda aka mika wa Tehran da Washington nan da nan, kuma ana sa ran ya fara aiki a ranar Litinin.

Shirin ya fara da bayyana bukatar tsagaita wuta nan da nan tare da bude mashigar Teku ta Hormuz, sannan a yi tattaunawa ta kwanaki 15 zuwa 20 don amincewa da Yarjejeniyar Islamabad.

“Dole a amince da dukkan bangarori a yau,” ta hanyar sanya hannu daga nesa kan yarjejeniyar fahimtar juna da Pakistan ta samar, kafa daya da bangarorin biyu ke tattaunawa da juna, in ji wani rahoto da Reuters suka fitar.

Tun a ranar Lahadi ne Axios suka rawaito cewa Amurka, Iran da masu shiga tsakani na yankin na tattaunawa don tsagaita wuta na kwanaki 45, wani bangare kenan na matakai biyu na kawo karshen rikicin gaba daya, suna masu rawaito majiyoyin Amurka da Isra’ila.

Sai dai kuma wani babban jami’in Iran ya fada wa Rueters a ranar Litinin cewa Tehran ba za ta bude Mashigar Hormuz ba saboda tsagaita wuta ta wucin gadi.

Jami’in ya tabbatar da cewa Tehran ta karbi daftarin na Pakistan kuma tana nazari a kansa, amma fa Iran ba ta son a takura wajen daukar mataki.

Bangare mafi girma na yarjejeniyar zai bukaci Iran da ta hakura da samar da makamin nukiliya inda za a janye mata takunkumai da sakin kadarorinta da aka daskarar.

Hadaddiyar Daular Larabawa mai arzikin man fetur a yankin kuma wadda yakın ya shafa sosai da makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka ta ce ya kamata amfani da Mashigar Tekun a koyaushe ya zama wani bangare na yarjejeniyar.

Kokarin yin sulhu

Iran ta zayyana matsayarta da bukatunta a sakon da ta aike don martani ga sakon neman tsagaita wuta da ta samu ta hannun masu shiga tsakani, in ji kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje ranar Litinin.

Kakakin Esmail Baghaei ya jaddada cewa ba za a iya cim ma matsaya tare da matsin lamba ba, yana mai cewa bukatun Iran sun samo asali ne daga manufofinta na kasa, kuma an mika su ta hanyoyin sadarwar da ake da su.

Baghaei ya kara da cewa Iran ta shirya martanintq da kanta a hukumance kuma za ta fitar da bayanai a lokacin da ya kamata.

A baya jami’an gwamnatin Iran sun nace kan samar da tsagaita wuta ta dindindin tare da bayar da tabbaci daga Amurka da Isra’ila kan cewa a nan gaba ba za su sake kai musu hari ba.

Dodon Nukiliya

Isra’ila, babbar abokiyar gabar Iran, a gefe guda na matsa lamba ga Amurka kan ta bar shirin Nukiliya na Iran da makamai masu linzami a cikin yarjejeniyar. Tel Aviv ta kuma ce ba za su daina kaiwa Lebanon hari ba ko da an cim ma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran.

Duk da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya, Trump ya sha bayyana cewa ana yin tattaunawa tsakanin Washington da Tehran.

Amurka ta mika wa Iran ta hannun Pakistan daftarin yarjejeniya mai gabobi 15, ciki har da bukatar Iran ta kawo karshen ayyukan samar da nukiliya inda za a janye mata wasu tatunkumai.

Da fari dai Tehran ta yi watsi da bukatun da aka mika mata ta hanyar masu shiga tsakani tana mai cewa ba ta tattaunawa da kowa, amma daga baya ta amince da shiga tattaunawar da Amurkawa.

Pakistan ta zama daya daga cikin masu shiga tsakani na kan gaba, tana mika bukatu ga Amurka da Iran, tana daukar nauyin tattaunawa a Islamabad, tare da hada kai da sauran abokai na yankin.

Turkiyya ma ta shiga aikin mika sakonni ga Amurka da Iran sosai, kuma ta shiga tattaunawa sa aka yi ta diflomasiyya tare da Pakistan, Masar da Saudiyya don cim ma tsagaita wuta da hana yakin yaduwa a yankin.

Makomar Hormuz

Dakarun Juyin Juya Hali na Iran sun sanar a ranar Lahadi cewa suna shirin samar da sabbin dokokin wuce wa ta Mashigar Teku ta Hormuz.

A wata sanarwa ta shafin X, dakarun ruwan Iran sun bayyana shirin ‘sabon tsarin Gabar Farisa’ a mashigar tekun mai muhimmanci.

Dakarun sun yi gargadin cewa sharuddan safarar kaya ta Mashigar Hormuz ba za su taba zama kamar yadda suke a baya ba, musamman ga Amurka da Isra’ila.

Tun bayan fara rikicin tsakanin Iran da Amurka-Isra’ila aka rufe hanya mafi girma ga jiragen ruwan kasa da kasa a ranar 28 ga Fabrairu.

Tun bayan fara rikicin Iran ta bayar da izini ga ‘yan jiragen ruwa kalilan don wuce wa ta Hormuz, inda suka kawo cikas ga daya bisa biyar na makamashin da ake bukata a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Oman ya rawaito cewa jami’an Oman da na Iran sun tattauna a ranar Lahadi da manufar sassauta kai komon jiragen ruwa a mashigar da ke rufe.

A kwanan nan ‘yan majalisar dokokin Iran sun  bayar da shawarar kafa cibiyoyin karbar haraji daga dukkan jiragen ruwan da za su wuce ta Hormuz.