Wildine: Mace mafi ƙanƙanta a duniya ta lashe kundin bajinta na Guiness na mai tallan kaya ƙawa
Wildine tana da matsalar SADDAN dysplasia, wani nau'in cutar gajarta wanda ba kasafai ake samunsa ba kuma dole ta yi yawo a cikin keken guragu. / Others
Wildine: Mace mafi ƙanƙanta a duniya ta lashe kundin bajinta na Guiness na mai tallan kaya ƙawa
A tsawonta da ya kai inci 2 ft 4 ko kuma 72cm, Wildine Aumoithe ta kuma lashe kundin bajinta na Guiness a matsayin wacce ta gajarrta a fannin kwararriya mai tallan katyan ƙawa a duniya.

Mace mafi ƙanƙanta a duniya wacce ke yawo da taimakon keken guragu mai sarrafa kansa, Wildine Aumoithe, ta kafa tarihi wajen samar da damammaki a guraben da babu wanda ya taɓa samu.

A tsawonta da ya kai inci 2 ft 4 ko kuma 72cm, ita ce mace mafi gajarta a fannin kwararriya mai tallan kayan ƙawa a duniya.

Sai dai waɗannan bajinta da ta lashe guda biyu na Guiness World Record suna ne da suka karaɗe kafafen watsa labarai. Ainihi labarin shi ne yadda take amfani da su.

An haife ta kuma ta girma a birnin Miami na Amurka ga iyayenta ‘yan asalin Haiti, Wildine tana da cutar SADDAN dysplasia, wani nau'in cutar gajarta wanda ya sa a mafi yawan lokuta take tafiya da taimakon keken guragu.

Bayan an haife ta a 2003, likitoci ba su yi zaton za ta iya rayuwa a bayan wannan daren ba.

'Mutum, mutum ne, komai ƙanƙantarsa'

Fast forward almost 23 years, and she is not just surviving; she is thriving and making sure other people feel seen.

Ga shi har ta kai shekaru 23, kuma ba wai kawai rayuwa take yi ba ; tana ci gaba tare da ba wasu mutanen dama.

Nasarorin da ta samu suna da yawa. Tana riƙe da kambun Guinness World Record guda biyu

Bayan da Guinness World Record ya tabbatar da ita a matsayin mace mafi ƙanƙwanta da ke rayuwa tare da taimakon keke mai sarrafa kansa a ranar 13 ga Oktoba 2021, ta bayyana cewa burinta shi ne "ƙarfafa wa mutane masu irin halittarta."

Kazalika a matsayinta na mace mafi gajarta a duniya, ta taɓa cewa "mutum mutum ne, komai ƙanƙantarsa".

Sannan a watan Satumba na 2023, an sake naɗa mata kambin bajinta na mace mafi gajarta a duniya a fannin kwararriya mai talla kayan ƙawa a duniya.

Wildine ta yi tattaki a makon dandalin New York Fashion Week, inda ta yi nuni da cewa kyau da takkan ƙaya ba su san girma ko tsayi ba.

‘Na ji daɗi da na kammala karatuna’

A Yanzu, ta ƙara wata girma a bajintar da take da su, inda ta kammala karatun digiri na farko a fannin Fasahar Zane-zane daga Jami'ar Liberty da ke Virginia a ranar 14 ga Mayu 2026.

"Na ji ɗaɗi da na kammala karatuna. Duk da cewa tafiyar ta yi tsawo, amma a ƙarshe an samu biyan buƙata. Kuma a yanzu ina jin ina da lokacin hutu," kamar yadda ta shaida wa GWR.

Kammala karatun ba shi ƙarshen abin da ta sa a gaba ba - shine farkon shirinta.

Wildine, wacce ke gudanar da tashar YouTube ɗinta da aka sani da Life Of Wildine inda take magana game da wakilcin masu fama da nakasa, ta kuma ƙaddamar da The Wild Creative Co., wani shafin kasuwanci da ta ƙirƙira mai zaman kansa, yayin da a bangare guda take sake mai da hankali kan yin tallan kayan ƙawa.

Yayin da take samun ci gaba, ba wai kawai tana alfahari da nasarorin da ta samu a matsayinta na mutum mai fama nakasa ba.

A lokuta da dama Wildine ta kan yi magana tare da alfahari game da wakiltar tsatsonta na Haiti da Baƙar fata da kuma alaƙar al'adu da tarihi na yankin ƙasar Caribbean da Afirka. Waɗanda take tafe da su ko ina ta je.

Kuma me yasa ta zama zakarar gwajin dafi ?

Saboda Wildine tana koƙarin ganin cewa baiwa ba ta zuwa daga siffa ko girman mutum kuma ta ƙi ta bar kowa ya fayyace mata abin da zai iya yiwuwa a rayuwarta.

A kalmominta: "iyakoki ba sa iya kayyaɗe abin da zai iya yiwuwa.’’