Ƙin karɓar fanareti: Kocin Man United ya yaba wa ɗan wasansa Dorgu

Kocin Manchester United, Ruben Amorim ya ce yana alfari da ɗan wasan ƙungiyar, Patrick Dorgu saboda ya nemi alƙalin wasa ya fasa bayar da fanaretin da ya ba su a wasansu da Real Sociedad.

/ AFP

Kocin Manchester United, Ruben Amorim ya yaba wa Patrick Dorgu, ɗan wasan ƙungiyarsu da ya nuna kyakkyawar halayya yayin wasansu da Real Sociedad a gasar Europa ranar Alhamis 13 ga Maris.

Dorgu ya nema alƙalin wasa ya soke hukuncin ba da fanaretin da ya yi ga Man United, lokacin da Real Sociedad suke ƙunci kan hukuncin alƙalin.

  • Ɗan wasan Real Sociedad, Aritz Elustondo ne ya kayar da Patrick Dorgu, lokacin da alƙali ya ba da fanareti ta farko a wasan da aka tashi 4-1, inda United ta doke Sociedad.
  • Dorgu wanda ɗan asalin Denmark ne mai tsatso a Nijeriya, ya ciyo wa ƙungiyarsa bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida a karo na biyu, lokacin da Hamara Traore ya tare shi a da’irar 18 ta ragar Sociedad.
  • Sai dai kuma, Dorgu ya je wajen alƙalin wasa inda ya masa nuni da hannayensa don cewa Traore ya karɓe ƙwallon bil haƙƙi, kuma ba laifin da ya cancanci fanareti ba ne. Nan-take aka warware hukuncin.
  • Kocin United, Ruben Amorim ya gaya wa ‘yan jarida cewa: "Ya danganta. Shi ne abin da ya dace, don haka ina matuƙar alfahari da shi amma ba zan iya cewa komai ba idan da sakamakon yana kan 0-0 ko kuma mu ne ke yin rashin nasara."
  • Kocin Real Sociedad, Imanol Alguacil bai ji daɗin aikin alƙalin wasan ba ɗan asalin Netherlands mai suna Benoit Bastien, wanda ya bai wa United fanareti har biyu sannan da jan kati ɗaya ga Sociedad.
  • Alƙalin ya kuma bai wa Real Sociedad fanareti lokacin da Matthijs de Ligt ya tare Mikel Oyarzabal, amma sai bayan an ce masa ya duba bidiyon abin da ya faru.
  • Kocin ya ce, "Mun so a ce alƙalin bai nuna son-kai ba. Bai kamata a mana alƙalanci irin wannan ba."
  • A yanzu dai Manchester United ce ba a taɓa dokewa a gasar Europa ta bana ba, kuma za su fuskanci Lyon a matakin kwata-fainal nan gaba.