Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) na shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin rai da rai da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa shugabanni biyu na ƙungiyar ta'addanci ta Ansaru, tana mai cewa hukuncin ya yi kaɗan idan aka yi la'akari da girman laifukan da suka aikata.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara'a, wanda ya ayyana kansa a matsayin Sarkin Ansaru, da kuma Abubakar Abba, wanda aka fi sani da Mahmud al-Nigeri, hukuncin ɗaurin rai da rai bayan sun amsa laifuka 32 da suka shafi ta'addanci.
Sai dai wani babban jami'in DSS ya ce hukumar za ta nemi kotu ta yanke hukunci mafi tsauri, yana mai cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin sun taka muhimmiyar rawa wajen sace ɗalibai da malamai a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo.

DSS ta kuma dage cewa an kashe malaman makaranta biyu ta hanyar fille musu kai a lokacin da ake tsare da su domin matsa wa gwamnati lamba.
Hukumar ta ce adalci ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu na buƙatar hukunci mafi tsauri fiye da ɗaurin rai da rai.
Usman ya riga ya amsa laifin haƙar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a bara, amma har zuwa ranar Litinin yana ƙalubalantar sauran tuhume-tuhume 31, waɗanda suka haɗa da ƙera na'urorin fashewa da kuma ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci.
Ɗora alhaki
Shugaba Bola Tinubu ya ɗora alhakin sace ɗaliban makaranta a Jihar Oyo a watan Mayu kan ƙungiyar Ansaru, wani ɓangare na Boko Haram da aka sani da gudanar da ayyukansa a tsakiyar Nijeriya har zuwa yankin Kudu maso Yamma.
An kuma danganta ƙungiyar da harin fasa gidan yari na Kuje a shekarar 2022, da ke wajen Abuja, da kuma harin da aka kai kan jirgin ƙasan da ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna a shekarar ta 2022.
An kafa ƙungiyar Ansaru a shekarar 2012, daga baya kuma ta haɗa kai da ƙungiyar Al-Qaeda. An sanar da kama Usman da al-Nigeri a watan Agustan 2025.
Gwamnatin ta ce an kama su ne a wani samame da aka kai a farkon shekarar.
Fashi da makami
Ana kuma kiran Usman da suna Abu Bara, yayin da ake kiran Al-Nigeri da Mallam Mamuda.
Ofishin Shugaban Ƙasa ya zargi mutanen biyu da hannu a wasu manyan sace-sacen mutane da aka yi a tsakiyar da arewa maso yammacin Najeriya, da kuma shirya hare-haren fashi da makami da dama.
Ofishin ya ce kuɗaɗen da suke samu daga waɗannan ayyuka suna amfani da su ne wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta'addanci. Sace ɗaliban makarantar a Jihar Oyo ya haifar da zanga-zanga.



















