Turkiya ta doke Kosovo inda ta samu damar shiga gasar cin kofin duniya ta 2026

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Turkiyya ta samu shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 da za a yi a Amurka da Mexico da kuma Canada a karo na uku a tarihinta .

By
Tawagar ƙwallon ƙafar Turkiyya ta samu shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 bayan ta doke Kosovo. / Reuters / Reuters

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Turkiyya ta samu nasarar shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 da za a yi a Amurka da Mexico da kuma Canada a karo na uku a tarihinta.

Turkiyya ta samu damar shiga gasar ne bayan ta doke Kosovo a wasan cike gurbi da ci ɗaya da nema.

Kerem Akturkoglu ne ya zura wa tawagar Turkiyya ƙwallo a raga minti 53 da fara wasa.

A wata sanarwa, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya taya tawagar, wadda aka sani da suna “‘ya’yanmu” murna kan samun shiga gasar.

Ya ce yana sa ran tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar za ta wakilci Turkiyya da sosai a fage mafi girma na ƙwallon ƙafa bayan shekara 24, yana mai nuna ƙwarin gwiwa cewa za su ɗauki launin ƙasar "daga nasara zuwa nasara " da kuma kasance abin alfahari ga ƙasar.

Erdogan ya kuma yi fatan yi wa tawagar fatan nasara a wasanninta na rukuni-rukuni da tawagogin ƙasashen Australia da Paraguay da kuma Amurka.

Turkiya ta samu shiga gasar cin kofin duniya sau biyu a tarihi.

Turkiyya ta fara shiga gasar ne a shekarar 1954, lokacin da suka fita a matakin rukuni ba tare da taka wata muhimmiyar rawa ba.

Gasar cin kofin duniya na biyu da Turkiyya ta shiga ya zo da wani sakamako na daban, inda Turkiyya ta kafa tarihi a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2002 , da ƙasashen Koriya ta Kudu da Japan suka karɓi baƙuncinta, inda ta zo ta uku cikin waɗanda suka yi fice a gasar.