Tallafin NATO ga Turkiyya zai gwada ƙarfin ƙawancensu yayin tashin hankalin Gabas ta Tsakiya: masana
Masu jawabi a zaman Faris sun yi gargaɗin cewa faɗaɗa rikici a yankin zai iya shafar tsaro da tattalin arzikin duniya.
Tallafin NATO ga Turkiyya idan tashe-tashen hankulan yanki suka yi ƙamari ba kawai zai goyi bayan Ankara ba ne, zai kuma gwada shirin ƙawancen, kamar yadda wani masanin tsaro ya bayyana ranar Laraba a wani taron tattaunawa a Faris kan dangantakar Turkiyya da ƙawancen NATO.
Murat Aslan, malami a jami’ar Hasan Kalyoncu kuma babban mai bincike a cibiyar SETA, ya yi gargaɗin cewa hare-haren Amurka da Isra’ila na kwanan nan kan Iran za su iya faɗaɗa kuma za su iya bazuwa zuwa yankin ƙasashen Larabawa.
Ya ce duk wani batun faɗaɗa rikicin zai shafi muradun Turkiyya da ƙawancen NATO.
Aslan ya kuma ce rikice-rikicen zamani suna haɗawa da arangama tsakanin gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu lamarin da ke buƙatar abin da ya kira “martani daban-daban” da ya haɗa da matakan soji da na siyasa.
‘Tsarin ƙasa da ƙasa bisa doka na cikin matsi’
Babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara Cagri Erhan ya ce tsarin ƙasa da ƙasa bisa doka da aka gina kan tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) bayan yaƙin duniya na biyu na fuskantar ƙarin matsin lamba.
Da yake magana a wajen tattaunawar, Erhan ya ce ababen da ke faruwa a duniya tun annobar Korona sun tura duniya zuwa wani lokaci na rashin tabbas mai barazanar tsaro da yanayin tattalin arziƙi mai rauni da kuma ƙarin matakan kare kasuwanni daga kayayyakin ƙetare.
Taron, wanda ofishin jakadancin Turkiyya a Faris ya shirya, ya haɗa kusan ‘yan jarida Faransa da na Turkiyya 30 domin tattauna dangantaka tsakanin Turkiyya da ƙawancen NATO da kuma abbubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya da kuma yaƙin Rasha da Ukraine.
“Tsarin ƙasa da ƙasa bisa doka na fama da hare-hare daga ko wane ɓangare,” in ji Erhan.
“A halin yanzu, babu wanda yake magana game da dokar ƙasa da ƙasa. Duk abin da ke kan teburin tattaunawa ya dogara ne kacokan kan muradun ƙasa. Babu wanda yake magana game da haɗin kai. Ba mu san irin sabon tsarin ƙasa da ƙasa da zai fito ba,” in ji shi.
Erhan ya kuma yi gargaɗin cewa yaƙin Rasha da Ukraine wani babban abin fargaba ne kuma yaƙin da ake tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran zai iya fi haka ƙamari.
Ya ƙara da cewa tsaiko a kasuwancin ƙasa da ƙasa da kuma hanyar rarraba kayayyaki ta duniya na ƙara fuskantar barazana.
Erhan ya ce Turkiyya ce za ta karɓi baƙuncin taron NATO da ke tafe a Ankara lamarin da zai haɗa shugabannin ƙasashen NATO da sauran abokan tarayya na ƙasashen ƙetare.
“A taron, za mu tattauna kan ƙarfafa tsaron NATO da haɗura na tsaro da ke tasowa,” in ji shi .
‘Abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya ba ya tsayawa a can’
Kilic Bugra Kanat, daraktan bincike na SETA a Washington, ya ce Turkiyya na da ƙwarewa wajen fuskantar rashin kwanciyar hankali da yaƙe-yaƙen basasa a kan iyakokinta, amma ya yi gargadin cewa hare-hare na baya bayan nan za su iya janyo rashin kwanciyar hankali mai girma a yankin.
Ya ce kashe kuɗi a kan tsaro tsakanin ƙasashen Gabas ta Tsakiya zai iya ƙaruwa ko ma an daina hare-haren.
“Idan rikicin ya ci gaba kuma ko wane nau’i na yaƙin basasa ya ɓarke a Iran, tasirinsa zai iya kasance mai girma,” in ji shi.
Kanat ya jaddada muhimmancin hana ƙarin taɓarɓarewar lamarin, yana mai cewa mutane a faɗin yankin sun gaji da shekarun rikici.
Ya ƙara da cewa hare-haren kwanan nan sun fara tasiri kan farashin makamashi kuma tasirinsu kan siyasa da zamatakewa da tsaro za su iya bayyana nan ba da jimawa ba.
“Abin da ya faru a Gabas Ta Tsakiya ba ya tsayawa a Gabas Ta Tsakiya . Mun ga wannan a sauran tashe-tashen hankula a Syria da Iraki,” in ji shi .