Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergey Lavrov ya ce ƙasashen Yamma na shirin yaƙi da Rasha, yayin da suke yaɗa abin da ya kira “ƙagaggen labari kan barazanar da ke fitowa daga Rasha”.
Lavrov ya ce a ranar Alhamis cewa Rasha za ta iya mayar da martani yadda ya kamata ga duk wata barazana da za ta shafi tsaronta daga waje.
“A yau, shugabanni da masu fada-a-ji a mafi yawan ƙasashen Yamma suna yaɗa wani ƙagaggen labari game da barazanar da ke fitowa daga Rasha, tare da yin shirin yaƙi da ƙasarmu,” in ji shi.
Lavrov ya bayyana hakan ne yayin buɗe taron ƙasa na huɗu na ƙungiyar International Russophile Movement a birnin Moscow.
Ya kuma zargi ƙasashen Yamma da sukar Moscow, ciki har da zargin cewa Rasha na lalata ƙa'idojin da suka shafi Turai.
Lavrov ya bambanta salon mu'amalar jami'an Amurka da na shugabannin ƙasashen Turai, yana mai cewa Washington a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Moscow ko da kuwa ɓangarorin biyu suna da matuƙar saɓanin ra'ayi.
“Akwai muhimmin bambanci tsakanin masu fada-a-ji a Amurka da na Turai. Su [Amurkawa] a shirye suke su tattauna. Ko da kuwa matsayinsu ya yi matuƙar saɓani da namu, tattaunawa tana da muhimmanci,” in ji shi.
Lavrov ya ce Moscow a shirye take ta yi tattaunawa mai ma'ana da jami'an ƙasashen waje waɗanda suke son shiga tattaunawa da gaske.
Ya kuma ce bai kamata jami'an ƙasashen waje su je Rasha domin kawai su maimaita sukar da suke yi wa ƙasar a bainar jama'a ba.














