Gwarzon ɗanwasan Barcelona, Robert Lewandowski ya bayyana cewa ya sauya salon rayuwarsa tun yana matashi, kuma hakan ne ya ba shi damar ci gaba da samun kuzari a shekarunsa yanzu.
Ɗanwasan mai shekaru 37 yana cikin mayan ‘yanwasan da ke nuna bajinta wajen zura ƙwallo da yanka a filin wasa. Kuma zuwa yanzu ya ci ƙwallaye kusan 400 a gasannin Turai.
Da yake bayani kan ƙarfin kuzarin da yake da shi, wanda yake taimaka masa wajen ci gaba da taka leda, Lewandowski ya ce ya daina cin kayan zaƙi da wasu nau’ukan abinci ne tun a baya.
Ƙarkon da Lewandowski ya yi a rayuwarsa ta ƙwallo ta samo asali ne tun yana matashi ɗan shekara ashirin da wani abu, lokacin da ya gane baiwa kaɗai ba za ta riƙe masa rayuwa ba.
Ya lura da nau’in kalacin safe da yake ci, wanda ya haɗa da kon fileks (corn flakes) da madara, wanda ke sanya masa kasala. Saboda haka ya sauya irin abincin da yake ci don rage sinadarin gluten da madara.
Kiyaye abincin da yake ci ya taimaka masa wajen mayar da hankalin kan kaifin tunaninsa, inda a yanzu yake cin ƙwallo duk bayan minti 96 a kakar La Liga ta bana.
Matarsa masaniyar abinci
A wata tattaunawa da wata jarida, Lewandowski ya ce ya saddaƙar daga cin kayan zaƙi, yana mei cewa,"Na yi tunanin saboda ba ni da ƙiba, wato ba ƙiba sai ƙwanji, zan iya ci gaba da cin cakuleti.
“Na ɗauka zan iya cin duk abin da na so [cakuleti da kayan zaƙi], saboda ba ni da wani kitse, amma idan na yi atisaye sai na ji ba ni da wani kuzari, kuma na kasa gane me ya sa. Ina bacci isasshe, amma ba na iya yin kamar abokan wasana. Don haka na fara yin sauyi. Bayan makonni kaɗan, na ga babban canji."
Baya ga jajircewar Robert Lewandowski, ɗanwasan ɗan asalin Poland ya jinjina wa matarsa, Anna, kan tallafin da ta ba shi har yake ci gaba da wasa yayin da tsaransa ke yin ritaya.
Anna dai tsohuwar ‘yarwasan kareti ce da ci lambobin yabo, kuma a yanzu ƙwararriyar masaniyar abinci mai gina jiki ce. Ta kasance tana taimakon Lewandowski wajen daidaita halayyar cin abincinsa.
"Ita ce babbar mai lura da lafiyar ƙwaƙwalwata, duk bayan wasa mai kyau ko mara kyau, ita ce farkon wadda nake magana da ita, game da wasan da ma ƙwaƙwalwata. Abin da nake tunani da yadda nake ji."
Duk da ƙoƙarinsa, a halin yanzu, Lewandowski na fuskantar rashin tabbas kan cigaba da zamansa a Barcelona, inda kwantiraginsa za ta ƙare a ƙarshen kakar 2025/26. A yanzu rahotanni na cewa ƙungiyar Chicago Fire ta Amurka na son ɗaukar sa.









