| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Mbappe da Vinicius za su koma aiki tare a wasan Real Madrid da Bayern Munich
Kocin Real Madrid na wucin-gadi, Arbeloa ya yanke hukuncin sake gwama Mbappe da Vinicius, bayan fuskantar matsin lamba kan buƙatar nuna bajinta a Gasar Zakarun Turai.
Mbappe da Vinicius za su koma aiki tare a wasan Real Madrid da Bayern Munich
Kylian Mbappe ya yi doguwar jinya kafin yanzu / Reuters
7 Afrilu 2026

A maraicen Talatar nan ne Real Madrid ta Sifaniya za ta kece raini da takwararta ta Jamus, Bayern Munich a gidan Madrid da ke Bernabéu, a zagayen kwatafainal ne na gasar Zakarun Turai ta 2025/26.

Wasan na zuwa ne a wani yanayi da ƙungiyar da ke zaman ta biyu a Gasar La Liga ke fama da matsin lamba, kasancewa alamu na nuna gasar La Liga tana gab da kuɓuce musu.

Koci Alvaro Arbeloa wanda ke aikin wucin-gadi a ƙungiyar mai girman tarihi, yana fuskantar ƙalubalen cewa lallai sai ya kai Madrid zuwa wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai, saboda shi ne kofin da ya rage musu da cikakken fatan samu.

Wasan Madrid na ƙarshe ranar Asabar ya zo da rashin sa’a inda ƙaramar ƙungiya a La Liga, Mallorca, ta doke su da ci 2-1, kuma sakamakon ya yi matuƙar janyo tababa kan ƙarewar koci Arbeloa da makomarsa a ƙungiyar.

Rashin nasara a gasar Zakarun Turai zai iya ta da hankalin shugabanni da masoya Real Madrid, waɗanda ba su saba ƙare kaka ba tare da kofi ba, musamman ma gasar Zakarun Turai da suka fi kowa lashewa a duniya.

Wasa da Bayern Munich

Ana sa ran wasan na yau zai sake gabatar da tagwayen taurarin Real Madrid, Kylian Mbappé da Vinicius Junior, inda za su ja ragamar gaban ƙungiyar, kamar yadda suka yi a baya.

Haɗakar ‘yanwasan biyu masu ji da kansu, kuma masu kamanceceniya a salon wasa ya kawo ƙalubale a baya, duk da cewa ana ganin zai haifar da babbar riba idan suka haɗa kansu.

Sai dai ana yawan maganganu kan dacewar aikinsu, da taimakekeniyar juna tsakaninsu. Amma a yanzu Arbeloa ya yanke shawarar sake gwama su bayan dawowar Mbappe daga doguwar jinya.

Baya ga Mbappe, akwai ɗanwasan da zai dawo tawagar, Federico Valverde, wanda ya kammala hutun dakatarwa, sannan akwai wani haziƙin, Jude Bellingham wanda ake sa ran ya murmure shi ma.

Ga jerin ‘yanwasan da ake sa ran za su take wasa a yau: Lunin; Trent, Rüdiger, Huijsen, Carreras; Valverde, Tchouaméni, Bellingham ko Pitarch, Güler; Mbappé, da kuma Vinicius.