Jirgin sama jannati mai zagaye sararin samaniya na farko da aka ƙera a Turkiyya zai fara aiki

Shirin FGN-TUG-S01 na Kamfanin Fergani Space zai harba jirgin sama jannati na farko da ake ƙera mai amfani da fetur da gas zuwa sararin duniya.

By
Jirgin sama jannati mai zagaye sararin samaniya na farko da aka ƙera a Turkiyya zai fara aiki / AA

Kamfanin Turkiyya Fergani Space ya ce na'urar harba jirgin sama jannati mai zagaye duniya da ake ƙera a ƙasar na (OTV) mai suna FGN-TUG-S01 ya fara aikinsa a sararin samaniya, a cewar wata sanarwa da aka fitar kwanan nan.

An ƙaddamar da na'urar harba jirgin sama jannati zuwa sararin samaniya na farko a Trukiyya a ranar 28 ga Nuwamba daga sansanin Vandenberg Space Force Base a California a kan roket din SpaceX Falcon 9 Transporter 15.

An kaddamar da aikin da misalin ƙarfe 6:44 na safe agogon GMT, kuma an yi nasarar kammala shi da raba kayan da aka ɗauka, bayan an ware na'urar daga roket ɗin minti 81 bayan ƙaddamarwa.

Wannan aiki ya zama muhimmin mataki ga ƙwarewar Fergani Space wajen jigilar kayan da kuma sarrafa zagaye a sararin samaniya.

Jirgin sama jannati na farko da aka yi amfani da shi a sararin samaniya na Turkiye ya ƙunshi injin roka na farko a duniya da aka harba a sararin samaniya. Jirgin zai yi aikin harba injinan hybrid na farko da aka tsara bayan ya sauka a sararin samaniya don aikin zagayensa.

Tsarin turawa na hybrid mai rahusa kuma mai aminci na FGN-TUG-S01 zai ba da damar ɗaukar tauraron ɗan’adam zuwa waɗansu duniyoyin daban-daban da kuma tsawaita lokacin aikinsu.

Nasarar wannan na'ura za ta zama sabon babban mataki ga ayyukan haɗin tauraron ɗan’adam na Fergani Space na gaba. Wadannan ayyuka za su haɗa da ajiye satelayiti a matakai daban-daban na lokaci mai tsayi.

OTV na cikin gida na farko a Turkiyya zai ɗauki tauraron ɗan’adam ɗin Fergani daga zagayen duniya a mafi ƙarancin kusan kilomita 500 zuwa wuraren da suka fi nisa fiye da kilomita 1,000 don sa su a cikin aikin zagayensu.

Na'urar tana ɗauke da mahimman tsarin kamar kwamfutar jirgi, na'urorin lantarki na tashi (avionics), na'urorin rarraba wutar lantarki, da tsarin kula da yanayin zafi, waɗanda duk a cikin ƙasar aka ƙera su a kamfanin Fergani Space.

Da wannan na'ura, Turkiyya za ta zama ƙasar farko da za ta yi gwaje‑gwajen injin hybrid a cikin orbita.

Selcuk Bayraktar, Shugaban Zartarwa (CEO) na Fergani Space, ya bayyana a wata sanarwa ranar Talata cewa kamfanin ya saka satelayit na biyu cikin aikin makonni uku da suka gabata kuma na'urar jigilar zagayen sararin saminiya da aka ƙera a ƙasar a yanzu tana aiki.