Rasha na karbar bakuncin kusan shugabannin Afirka ashirin a Moscow a ranakun Laraba da Alhamis din nan.
Moscow ta daɗe tana ƙulla alaƙa da Afirka tun zamanin Hadaddiyar Daular Soviet, kuma ta daɗe tana kallon nahiyar a matsayin wani abu da zai mayar da martani ga abin da take gani a matsayin mamayar ƙasashen yamma a kan harkokin ƙasashen duniya.
"Mu ƙawaye ne na halitta wajen gina tsarin duniya mai ra'ayin mazan jiya da yawa," in ji mataimakin Kremlin Yuri Ushakov game da taron, yana mai nuni da cewa gwagwarmyar karfin ikon siyasa ba ya ƙara ta'azzara a Yammacin duniya sai dai cikin wasu yankuna da dama.
An shirya cewa wakilai daga ƙasashen Afirka 48 za su halarci taron, kuma 22 daga ciki za su samu wakilcin shugabanninsu, in ji Ushakov.
Sanarwar da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kan abin da ya kira "mulkin mallaka na zamani" a nahiyar ya yi tasiri ga wasu shugabannin Afirka, musamman tsaffin yankunan mulkin mallaka na Faransa a yankin Sahel.
Hadin kan tattalin arziki
Daga cikin shugabannin da aka tsara Putin zai gana da su akwai takwaransa na kasar Mali, Assimi Goita, wanda gwamnatinsa ke hadin gwiwa da sojojin haya na Rasha wajen yaki da ta'addanci.
Ushakov ya ce za a kuma gudanar da tarurruka na baki daya inda "dukkan shugabannin tawagogi za su samu damar yin magana."
A cewar fadar Kremlin, za a sanya hannu kan takardu guda 33 a yayin taron, wadanda wasu daga cikin su suka shafi hadin gwiwa a fannin tattalin arziki.
Haka kuma, Rasha za ta yi kokarin karfafa kasancewar ta a fannin diflomasiyya a nahiyar Afirka.















