NATO na fuskantar ‘mummunar makoma’ idan ƙasashenta suka ƙi taimaka wa Amurka a yaƙin Iran - Trump
Trump ya ce yana sa ran ƙasashe ƙawayen Amurka za su ba da tasu gudunmawar a Mashigar Hormuz, kamar yadda Amurka ta taimaki Ukraine a yaƙin da take yi da Rasha.
Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ƙungiyar NATO na fuskantar makoma “mummuna” idan har ƙasashen da ke ƙawance da Amurka suka gaza taimakawa wajen buɗe Mashigar Hormuz (Strait of Hormuz), wata muhimmiyar hanyar sufurin mai wacce Iran ta rufe.
A wata taƙaitacciyar hira da ya yi da jaridar The Financial Times (FT) a ranar Lahadi, Trump ya ce kamar yadda Amurka ta taimaki Ukraine a yaƙin da take yi da Rasha, haka shi ma yake sa ran ƙasashen Turai za su taimaka a kan Mashigar Hormuz, wanda rufe shi ya sa farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabi a faɗin duniya.
“Idan ba a mayar da martani ba, ko kuma idan martanin ya kasance mara kyau, ina jin hakan zai yi matuƙar illa ga makomar NATO,” in ji Trump, wanda tsawon shekaru yana sukar ƙawancen da cewa wasu ƙasashe suna cin moriyar dukiyar Amurka ba tare da bayar da tasu gudunmawar ba.
Trump ya ƙara da cewa, “Ya dace mutanen da su ne masu cin gajiyar wannan mashigar su taimaka wajen tabbatar da cewa babu wani mummunan abu da ya faru a wurin.”
Yayin da aka tambaye shi game da takamaiman taimakon da yake buƙata, Trump ya gaya wa FT cewa yana son jiragen ruwa masu kwashe bama-bamai da nakiyoyi na cikin ruwa da kuma “mutanen da za su fatattaki wasu miyagun mutane da ke gaɓar tekun [Iran].”
Game da batun yarjejeniya da Iran
Trump ya ce yana tattaunawa da ƙasashe bakwai game da yadda za a tabbatar da tsaron a Mashigar Hormuz.
Kazalika ya bayyana cewa Amurka tana tuntuɓar Iran, amma ya nuna shakkun ko ƙasar a shirye take don yin da tattaunawa don kawo ƙarshen rikicin.
Trump ya gaya wa manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One cewa gwamnatinsa tana magana da Iran, “amma ba na jin sun shirya.”
Rashin tabbas game da tsawon lokacin da yaƙi da Iran zai ɗauka ya girgiza kasuwannin mai, inda farashin ɗanyen mai ya yi tashin gwauron zabi a cikin makonni biyun da suka gabata sakamakon fargabar katsewar kayayyaki.
A ranar Lahadi, farashin ɗanyen mai nau’in (West Texas Intermediate na Amurka) ya tashi da kaso 2.5 cikin 100 a kan $100.22 kan kowace ganga, yayin da farashin ɗanyen mai na Brent ya tashi da kashi 2.9 cikin 100 zuwa $106.11 kan kowace ganga.