Kashe-kashen RSF a Al Fasher na Sudan kisan ƙare-dangi ne: Rahoton MDD
Masu bincike sun gano hujjar kai hare-hare na kabilanci da kuma da dabarun ƙaƙaba yunwa da kuma cin zarafi na jima'i - muhimman shika-shikan laifin kisan kiyashi a ƙarƙashin dokar ƙasa da ƙasa - a lokacin da RSF ta karɓe iko da Al Fasher.
Kashe-kashen al’ummomin da ba Larabawa ba a lokacin da rundunar RSF ta ƙwace birnin Al Fasher na Sudan yana cika shika-shikan kisan kiyashi, in ji wani bincike mai zaman kansa na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a wani sabon rahoton da aka fitar ranar Alhamis.
A ƙarshen watan Oktoba na shekarar da ta gabata, RSF ta karbe iko da birnin, wanda ya kasance wuri na ƙarshe da sojin Sudan (SAF) ke da ƙarfi a yankin Darfur a yammacin ƙasar, inda aka kashe tare da yi wa dubban mutane fyaɗe a lokacin kwanaki uku na tashin hankali, in ji tawagar ƙasa da ƙasa ta bincike ta MDD a Sudan.
Ya biyo bayan wata ƙawanya ta watanni 18 inda rundunar RSF ta ƙaƙaba yanayi da zummar lalata al’ummomin da ba na Larabawa ba, musamman al’ummomin Zaghawa da Fur, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Tawagar ta MDD ta ce ta gano hujja cewar RSF tana kai hare-hare kan mutane bisa ƙabilarsu da jinsi da kuma abin da ake tunanin ra’ayoyinsu na siyasa, ciki har da kashe-kashe mai yawa da fyaɗe tare da ƙaƙaba wani yanayi da zummar lalata al’ummar, wani muhimmi ne daga cikin shika-shikan laifin kisan kiyashi a dokar ƙasa da ƙasa.
Rundunar RSF ba ta mayar da martani ba ga buƙatar da tawagar MDD ta neman ganawa da shugabanninta, in ji rahoton.
Rundunar RSF da sojin Sudan ba su mayar da martani ba nan take ga buƙatar da kamfanin dillancin labaran Reuters ta yi ta neman ta yi tsokaci.
A baya dai, rundunar RSF musanta yin irin wannan cin zalin, tana mai cewa maƙiyanta ne suka ƙirƙiri labarin inda ta yi zarge-zarge a kansu.
"Mataki da yadda aka tsara da kuma yadda manyan jami’an suka RSF suka amince da ayyukan a bayyane ya nuna cewa laifukan da aka aikata ciki da kuma kusa da Al Fasher ba wai wuce gona da iri na yaƙi ne kawai ba," in ji Mohamad Chande Othman, shugaban tawagar binciken ƙwaƙwaf a kan Sudan.
"Sun kasance wani ɓangare na ayyukan da aka shirya da ake da alamu na laifin kisan kiyashi," in ji shi.
Kafin a ƙwace iko da shi, mutanen da ke cikin birnin Al Fasher sun ƙunshi ‘yan ƙabilar Zaghawa, wata ƙabilar da ba Larabawa ba ne, ysayin da sansanonin ‘yan gudun hijira kusa da wurin sun ƙunshi ‘yan ƙabilar Fur da Berti da Masalit da kuma Tama, in ji rahoton.
‘Maganganun kisan ƙare dangi’
"Wadanda suka tsira sun bayyana barazana ƙarara na ‘share’ birnin," in ji rahoton.
Baya ga kai hare-haren kan sansanonin ‘yan gudun hijira da wuraren dafa abinci na jama’a da cibiyoyin kiwon lafiya da jirage mara matuƙa da manyan makamai, RSF ta kuma yi kashe-kashe da ƙwace da cin zarafi a Al Fasher, in ji rahoton.
“Kalamun ƙare-dangi” na RSF da sauran laifuka sun nuna niyyar ɗaiɗaita ‘yan ƙabilar Zaghawa da Fur gaɗaya ko kuma wani ɓagare, in ji rahoton.
"Shaidu sun ji dakarun RSF suna cewa, 'shin akwai wani Zaghawa a cikinku? Idan muka samu Zaghawa, za mu kashe su gabaɗaya '," in ji rahoton.
Waɗanda suka tsira sun ba da labarin kisan gilla kan fararern hula tare da kasancewa gawargwakin maza da mata da ƙanana yara sun cika hanya, in ji rahoton.
An yi fyaɗe da sauran matakai na cin zarafi tare da duka da tuɓewa ala tilas wa mata da yara masu shekaru 7 zuwa 70 daga al’ummomin da ba Larabawa ba ne, musamman a kan Zaghawa, in ji rahoton.
"Abubuwan da wannan rahoton na MDD ya gano amasu ɗaga hankali da cin zarafi ciki har da tsarin ƙaƙaba yunwa da cin zarafi da kashe-kashe da fyaɗe da kuma kai hari kan wata ƙabila da gangan da ya kai wani mataki mai tsanani a lokacin da RSF ta yi wa Al Fasher ƙawanya," in ji sanarwar.
Mambobin ofishin kare ‘yancin ɗan’adam na MDD ne suka bai wa tawagar ta MDD ta ce aikin binciken cin zarafin a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa a ciki da wajen Al Fasher bayan samun goyon bayan ƙasashe irin su Birtaniya.