UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi

Kimanin kashi 73.7 na mata "ba su da isasshen abinci mai gina jiki, abin da ke nuna matsanancin halin da suke ciki kuma yana ta'azzara yiwuwar fama da tamowa," in ji shirin UN Women.

By
Mutanen da aka raba da gidajensu a Al Fasher suna cikin waɗanda ke fuskantar uƙuba

Shirin da ke kula da harkokin mata na Majalisar Ɗinkin Duniya, UN Women, ya yi kira a ɗauki matakin gaggawa domin kare mata da ‘yan mata a Sudan, inda yaƙin da ake yi yake ta’azzara baƙar yunwar da ta shafi miliyoyin mutane.

"An kwashe fiye da shekaru biyu a fagen daga a Sudan lamarin da ya kassara rayuwar mata da ‘yan mata da raba su da gidajensu da makomarsu, inda suke ɗanɗana kuɗarsu sakamakon wannan babban bala’i na rikicin Sudan," a cewar Anna Mutavati, daraktar Gabashi da Kudancin Afirka ta Shirin UN Women, a hira da manema labara a Geneva ranar Talata.

Alƙaluman da UN Women ya fitar game da yanayin samun abinci da rashin tsaro a Sudan sun nuna cewa mata da ‘yan mata kimanin miliyan 11 na fama da matsanancin ƙarancin abinci.

"Kasancewa mace a Sudan wata babbar alama ce ta fuskantar yunwa," in ji Mutavati.

Ta ƙara da cewa a yayin da yaƙi yake ƙamari a Al Fasher sannan ake ci gaba da fama da ƙarancin abinci a faɗin Darfur, mata da ‘yan mata suna fuskantar "matsananciyar yunwa da kora daga gidajensu da kisa da lalata da musgunawa."

Lamarin ya ta’azzara ne bayan a hukumance an ayyana yankin Al Fasher da Kadugli a matsayin wuraren da ke fama da matsananciyar yunwa a watan Nuwamba.

MDD ta yi kira a yi gaggawar taimaka wa mata

Bayanan da shirin UN Women ya fitar sun nuna cewa Kimanin kashi 73.7 na mata "ba su da isasshen abinci mai gina jiki, abin da ke nuna matsanancin halin da suke ciki kuma yana ta'azzara yiwuwar fama da tamowa."

Mutavati ta jaddada buƙatar gaggawa ta tabbatar da ganin an bai wa mata da ‘yan mata agajin jinƙai da suka shafi buƙatunsu, tana mai cewa su ne suka fi galabaita a yaƙin Sudan.