| Hausa
TATTALIN ARZIKI
2 minti karatu
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
Da yake magana a yayin ganawar tawagar da shi, shugaban ƙasar ya ce “za a gyara NNPC a kuma sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya”.
Za a gyara kamfanin NNPC tare da sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya —Tinubu
NNPC ne babban kamfanin man Nijeriya

Shugaban Bola Tinubu na Nijeriya ya ce za a gyara kamfanin man Nijeriya (NNPC) tare da sayar hannayen jarinsa a kasuwar hanneyn jarin Nijeriya.

Tinubu ya bayyana wannan ne ranar Alhamis a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin kasuwar hannayen jarin Nijeriya (NGX).

Shugaban kasuwar NGX Umaru Kwairanga da kuma Babban Daraktan Kasuwar Temi Popoola ne suka jagoranci tawagar kasuwar zuwa fadar gwamnatin Nijeriya a Abuja.

Da yake magana a yayin ganawa da tawagar, shugaban ƙasar ya ce “za a gyara NNPC a kuma sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya”.

Tinubu ya ce kalamai kyawawa daga masana tattalin arziki da kuma alƙaluma masu ba da ƙwarin gwiwa sun nuna wata makoma mai kyau ga dukkan ‘yan Nijeriya.

A ranar 12 ga watan Yuli, Bayo Ojulari, Shugaban Kamfanin Man ya bayyana cewa kamfanin na shirin fara sayar da hannayen jarinsa a kasuwar hannayen jarin Nijeriya nan da shekarar 2028.

“Tare da haɗin gwiwar abokan aikinmu a masana’antar, za mu kasance waɗanda za su sauya kamfanin man ƙasa zuwa kamfani mai zaman kansa [wato Limited Liability Company a Ingilishi],” kamar yadda shugaban NNPC ɗin ya bayyana.

“…Muna da tsarin kasancewa cikin waɗanda ake sayar da hannayen jarinsu nan da shekarar 2028.”

Ojulari ya ce NNPC ta samu “gagarumin ci-gaba ” wajen samar da wani yanayi na kasuwanci mai ɗorewa da aminci a Nijeriya.

Shi ma, da yake bayani yayin ziyarar, shugaban Hukumar Tara Harajin Nijeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya ce cire tallafin man fetur ne ya shimfiɗa tubalin gyara gurɓacewar abubuwa da suka shafi ƙasar cikin shekaru 40 suka gabata .

Ya ce ƙwarin gwiwar cire tallafin, ƙasa da sa’a ɗaya bayan rantsuwar kama aiki “shi ne ginshiƙi da tubali da muhimmnin abin da ya janyo sauye-sayen da muke gani”.