Kutungwilar Netanyahu kan tsagaita wuta a Gaza ita ce ci gaba da kashe Falasdinawa
Sabbin hare-haren Isra’ila a yankin da aka mamaye ba bayyana manufar kasar Yahudawa ta ci gaba da aikata kisan kiyashi, har ma a lokacin da a baki ta ce tana aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Da yammacin ranar Talata, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ba da umarnin a sake kai sabbin hare-hare a Gaza, yana mai ikirarin cewa kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta.
Batun dai ya sakasance irin wanda aka saba da shi: ayyana keta doka a bainar jama'a, ikirarin bukatar sojoji, da kuma sanarwar mayar da "martani".
Duk da haka babu daya daga cikin wannan da ya ɓoye gaskiyar lamarin: kisan kare dangi bai tsaya ba.
An kashe Falasdinawa sama da 100 a cikin makonni bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta. Kuma a cikin sabon rikicin, Isra'ila ta kashe mutane 104 a cikin dare ɗaya kaɗai - ciki har da aƙalla yara 35.
Ga mutanen Gaza, bama-bamai sun tsaya na ɗan lokaci, amma kisan rayyukansu ya ci gaba. Abin da duniya ta shaida ba tsagaita wuta ba ne. Lokaci ne na ɗan tsahirtawa don ruguza rayuwar fararen hula da aka dana wa tarko.
Netanyahu kawai yana neman uzuri ne don sake fara aiwatar da cikakken aikin kisan kare dangi.
Gwamnatinsa ba ta taɓa ɓoye wannan buri ba. Ministoci masu ra'ayin mazan jiya kamar Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich sun sha nuna buƙatar a koma ga kai manyan hare-haren bama-bamai da ma kai hare-hare ta ƙasa.
Suna bayyana du wani jinkirin da ake samu na faɗaɗar sojoji a matsayin rauni, har ma da cin amana. Waɗannan ba masu tayar da zaune tsaye ba ne, manyan jami'ai ne da ke jagorantar manufofin.
Matsin lambarsu tsayayyiya ce kuma saƙonsu a bayyane yake: Dole ne Gaza ya ci gaba da zama wajen kai hari. Babu wata tsagaita wuta, komai rauninta, daza a ce an samar wai da nufin kawo zaman lafiya.
Isra'ila ta dage cewa waɗannan sabbin hare-haren mayar da martani ne, waɗanda ayyukan Falasɗinawa suka tilasta kai wa.
Amma tarihi ya nuna cewa ƙasar da ta himmatu wajen lalata wasu mutanen, ba ta cika gwagwarmayar neman hujja ba.
Idan ana ci gaba da kisan kare dangi, samun hujja da dalili sun zama aiki. A sanya wa wadanda abin ya shafa sunan barazana. A samar da bukatar kare kai. A gabatar da tashin hankali mai girma a matsayin bukata ta rashin son rai.
Sannan sai a dogara ga manyan kasashen duniya don su yi tsayin daka.
Yakin Netanyahu da ba ya zuwa karshe
Dakatar da wannan kisan kare dangi zai bukaci shugabannin Isra'ila su fuskanci daukar alhaki na siyasa da na shari'a.
Netanyahu yana fuskantar matsin lamba mai yawa a cikin Isra'ila saboda gazawar da ya yi a baya. Tsagaita wuta ta dindindin zai shafi tunanin cewa yaki mara iyaka yana da amfani ga Isra'ila ko tsaronta. Zai fallasa munanar dabi'a a zuciyar mulkinsa.
Ci gaba da aikata kisan kare dangi ya zama sulkensa na siyasa.
Muddin Falasdinawa suna mutuwa, tattaunawar jama'a a cikin Isra'ila ta ci gaba da mai da hankali kan tatsuniyar "nasara" maimakon gaskiyar bala'in da ke faruwa.
Yayin da waɗanda ke kan mulki ke yin waɗannan wasannin na siyasa, mutanen Gaza suna fuskantar sakamako kawai.
Kwanakinsu a ƙarƙashin tsagaita wuta ba na aminci ba ne. Gudun hijira ya kasance kamar yadda yake ba sassautawa. Yunwa ta ƙaru. Ruwa mai tsabta har yanzu yana ƙaranci. Asibitoci ba su da kayan aiki.
Yara suna yin barci ba tare da sanin ko za su farka ba. Fararen hula sun mutu sakamakon raunukan da ba a yi wa magani ba, cututtuka masu warkewa, da yunwa.
Rashin bama-bamai bai kawo samuwar rayuwa ba. Har yanzu ana ci gaba da rayuwa a ƙarƙashin mamaya a matsayin wani nau’i na tashin hankali.
Magoya bayan Isra'ila a ƙasashen waje na ci gaba da jaddada taka tsantsan da samar da daidaito a cikin harshensu na kalami a tsakanin jama'a. Suna kira da a yi taka tsantsan yayin da suke ba da makamai. Suna nuna damuwa yayin da suke ba da kariya ta diflomasiyya. Sabani yana fitowa karara.
Idan da gaske kasashen duniya sun yi imanin cewa dole ne a dakatar da kisan kare dangin, da sun daina bayar da damar aikata hakan. Idan rayukan Falasdinawa na da daraja, da martanin zai nuna gaggawar magance kashe-kashen.
Tazara tsakanin maganar baki da aiki a aikace na bayyana hadin baki.
Kowane sabon hari yana ƙara zurfafa wannan tabo. Harin da aka kai da daddare na ranar Talata ya tabbatar da wani abu da ya kamata ya kasance a bayyane tun da daɗewa. Babu wani alƙawarin zaman lafiya.
Kawai dai an yi ɗan hutu na dabarun sake shiri, sake tattara kayan aiki, da kuma tabbatar wa abokan hulɗa cewa Isra'ila har yanzu tana aiki a cikin tsarin "halascin ƙasa da ƙasa".
Kisan kiyashi da sunan tsagaita wuta
Netanyahu da ministocinsa sun yi magana a fili game da niyyar da ya kamata ta tsoratar da kowace al'umma da ke iƙirarin daraja haƙƙin ɗan adam.
Shiri da manufarsu a Gaza ba su da digon da aminci, mutunci, ko 'yanci ga mutanen yankin.
Manufarsu ta haɗa da mamaya, korar mutane, da ruguza su. Suna magana kamar cewa Falasɗinawa kalubale ne ba wai mutane ba. Wadannan kalami na ƙirƙirar duniya inda za a iya musanta aikata kisan kare dangi ko da yake yana aikata hakan da tsakar rana.
Tsagaita wuta da a karkashinta har yanzu ake ci gaba da kashe rayuka ba tsagaita wuta ba ce. Kalami ne na bayar da kariya ga bala’o’i.
Tsagaita wutar na ba wa jami'an diflomasiyya damar jin suna da amfani a yayin da fararen hula ke zubar da jini. Tana samar da kanun labarai na "cigaba" yayin da iyalai ke tono kaburbura. Tana tabbatar wa masu sanya idanu daga nesa cewa ana kawar da rikicin.
Tambayar da duniya za ta fuskanta yanzu abu ne mummuna amma mai sauƙi.
Sau nawa za a bar Isra'ila ta sake dawo da aikata wannan kisan na kare dangi kafin a daina amfani da kalmar "tsagaita wuta" wajen bayyana dakatarwar?
Me ma ake ɗauka a matsayin zaman lafiya a wurin da rayuwa kanta take zama kokarin juriya da tirjiya?
Har yanzu akwai lokaci don bayar da amsoshin da suka sha bamban da wadanda aka bayar zuwa yanzu.
Duk da haka kofar na rufewa. Kowane sabon tashin bam na ƙara rufe kofar. Kowane rai da aka rasa na bayyana gaggawar d aake bukata. Dole ne ƙasashen duniya su fuskanci abin da suke bayar da dama ake aikata wa. Ba gobe ba. Ba bayan zagaye na gaba na tattaunawa ba. Yanzu.
Domin idan wannan shi ne abin da duniya ke kira tsagaita wuta, wace kalma ce ta rage wa kisan kare dangi?