| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
An kashe sojoji 8 a wani harin wata ƙungiya mai alaƙa da Daesh a arewa maso gabashin Nijeriya
'Yan ta'adda sun kai hari a wani sansanin soji a jihar Borno, in ji jami'ai.
An kashe sojoji 8 a wani harin wata ƙungiya mai alaƙa da Daesh a arewa maso gabashin Nijeriya
Sojojin Nijeriya suna kan gaba wajen yaƙi da 'yan ta'addan Boko Haram
13 awanni baya

An kashe sojoji takwas ranar Laraba a wani hari da wata ƙungiyar ta’addanci mai alaƙa da Daesh- ISWAP- ta kai a arewa maso gabashin Nijeriya, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka ruwaito.

Wani jami’in soji ya ce mayaƙan ISWAP sun kai hari kan wani sansanin soji a ƙauyen Kauwa na jihar Borno.

Jami’in ya ce sojoji 23 sun ji jikkata a harin.

Nijeriya ta shafe shekaru tana fama da hare-hare daga ƙungiyoyin  ‘yanta’adda  da ‘yanbindiga, ciki har da ‘yan Boko Haram da ISWAP, a sassan ƙasar.