| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Kotu a Nijeriya ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa kan harin Cocin Owo na 2022
A hukuncinsa, Mai shari’a Nwite ya same su da laifi a kan dukkan tuhume-tuhumen tara da suka shafi aikata ayyukan ta’addanci da suka saɓa wa Dokar Hana da Rigakafin Ta’addanci.
Kotu a Nijeriya ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa kan harin Cocin Owo na 2022
Cocin Owo na Jihar Ondo / Others

Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke wa wasu mutum huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin kai harin ranar 5 ga Yunin 2022 a Cocin Katolika na Saint Francis da ke Owo a Jihar Ondo.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin na cikin mutane biyar da ake tuhuma da laifukan ta’addanci guda tara da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Nijeriya (DSS) ta shigar a kansu dangane da harin da aka kai wa cocin, inda aka kashe fiye da masu ibada 40 tare da jikkata sama da mutum 100.

Sai dai wanda ake tuhuma na biyar, Momoh Otuho Abubakar mai shekaru 47, kotun ta wanke shi tare da sallamarsa daga tuhumar.

Hukuncin ya zo ne a daidai lokacin da Nijeriya ke ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci, wata barazana da ta daɗe tana addabar al’ummomi a sassa daban-daban na ƙasar ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

A hukuncinsa, Mai shari’a Nwite ya same su da laifi a kan dukkan tuhume-tuhumen tara da suka shafi aikata ayyukan ta’addanci da suka saɓa wa Dokar Hana da Rigakafin Ta’addanci.

Daga cikin laifukan akwai kasancewa mambobin wata ƙungiyar ta’addanci da aka haramta, Al-Shabab (wadda aka ce tana da alaƙa da ISWAP), haɗa baki domin aikata ta’addanci, garkuwa da mutane, tsare su da kuma kashe fiye da masu ibada 40.

Mai shari’ar ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa waɗanda aka yanke wa hukunci ba tare da wata shakka ba.

Sai dai ya ce ɓangaren masu gabatar da ƙarar ya gaza tabbatar da tuhuma a kan wanda ake zargi na biyar, wanda hakan ya sa aka wanke shi.

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da yawa suka jikkata lokacin da wasu masu ɗauke da makamai suka buɗe wa masu ibada wuta a cocin da ke hedkwatar ƙaramar hukumar Owo ta Jihar Ondo.

Lamarin ya jawo Allah-wadai daga sassa daban-daban na ƙasar, inda mutane da ƙungiyoyi suka yi kira ga gwamnati da ta kamo waɗanda suka kai harin tare da tabbatar da an hukunta su.

Rumbun Labarai
ICPC ta miƙa filin ginin gidaje 962 na aikin dala miliyan 65 ga Bankin Lamunin Gidaje na Nijeriya
Matatar Dangote ta koma sayar da fetur a naira, ta ƙara farashin lita da N140
Trump ya yabi Tinubu kan 'jagorancinsa a yaƙi da ta'addanci' a Nijeriya
Nijeriya ta kaddamar da shirin takardun lamuni na N729bn don biyan basussuka a fannin lantarki
An yi garkuwa da fiye da mutum 40 a hare-haren 'yanbindiga a Jihar Zamfara
NESREA ta fara bincike kan zargin zubewar sinadari a babbar hanyar Kaduna-Abuja
Jami’an tsaron Nijeriya sun kama ɗanta’adda ɗan ƙasar Sudan da wata mace ‘yar Ghana a Borno
DSS ta Nijeriya za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yanke wa shugabannin Ansaru
Ana fargabar mutane 40 sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a jihar Jigawa a ke Nijeriya
An kashe wasu ɗalibai yayin da sojoji suka daƙile yunƙurin 'yanta'addan Daesh na sace su a Borno
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutum 12 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Benue
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da shirye-shiryen ayyukan Bankin Duniya na dala biliyan 3.05
Fiye da mutum 1,000 ne suka tsere wa hare-haren 'yanbindiga a jihar Benue ta Nijeriya
Kotun Nijeriya ta ba da umarnin ƙwace kadarorin Aisha Achimugu na kusan Naira biliyan 9
Sojojin Nijeriya sun kama 'yan ƙasashen waje 24 a wani samame a Jihar Legas
Wata kotu a Kano ta hukunta wanda ya tallata wiwi a intanet da zaman yari na shekaru 7
‘Yansandan Nijeriya sun bazama don ceto ɗaliban da aka sace suna rubuta jarrabawar NECO a Kogi
Nijeriya za ta jagoranci tallafin jinƙai yayin da tsarin tallafin MDD yake sauyawa, a cewar minista
'Yansandan Nijeriya sun kama Adeniyi wanda ake zargi da kafa hukumar bogi
Nijeriya da Masar na shirin karfafa hadin gwiwa a yaki da miyagun kwayoyi