Tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger, wanda babban jami’i ne a hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA ya yi tsokaci kan yunƙurin da shugaban FIFA, Gianni Infantino ya yi na sayar da hannun-jarin gasar Kofin Duniya.
Wenger ya nisanta kansa daga shirin na shugaba Infantino wanda bai yi nasara ba. Sannan ya ce “ya wajaba matuƙa” a yi watsi da shirin saka ‘yankasuwa a babbar gasar.
Sanarwarsa ta ranar Talata na zuwa ne bayan da hukumar ƙwallo ta nahiyar Turai, UEFA ta yi watsi da shirin Infantino gabaɗayansa, kuma ta janye goyon baya gare shi a zaɓen shugabancin FIFA na baɗi.
“Ba ni da hannu cikin shirin kuma na fara jin labarin batun ne ta hanyar rahotannin ’yanjaridu,” in ji Wenger, wanda Infantino ne ya ɗauke shi aiki a 2019 inda ya zama babban jami’in FIFA kan cigaban ƙwallon ƙafa.
Wenger ya ƙara da cewa, “Matakin janye batun ya wajaba matuƙa saboda na yi amanna da ‘yancin-kan FIFA da ke hidima ga wasanmu cike da himma, bayyana gaskiya, da nagarta”.
Sai dai sanarwar ta Wenger ba ta ambaci sunan Infantino ba, kuma ta zo a makare saboda an ɗauki kusan mako guda ana ɓaɓatu a duniyar ƙwallo kan batun.
Ayyukan Wenger a FIFA
Tuni dai a ranar Asabar da ta gabata Infantino ya janye ƙudurinsa na kawo masu zuba jarin dala biliyan $20, sakamakon mummunar suka daga jami’an ƙwallo a duniya da hukumomin ƙwallo, ciki har da UEFA wadda ta yi barazanar ƙaurace wa gasanni na bukukuwan FIFA.
Ƙudurin ya yi niyyar kafa wani kamfani mallakin FIFA, mai suna FIFA Forward Enterprise (FFE), don gudanar da ɓangaren neman kuɗi, kasancewar hukumar FIFa ba ta aikin neman riba.
Babban kamfanin zuba jarin da aka ayyana shi ne “Thrive Eternal”, wanda Joshua Kushner ya kafa, wanda shi kuma ɗan’uwa ne ga Jared Kushner, suruki ga shugaban Amurka, Donald Trump.
A yunƙurin cimma ƙudurin, FIFA ta yi tayin ba da dala miliyan $20 ga kowanne cikin hukumomin ƙwallo 211 da ke zaman mambobinta, kuma mamallakanta a dokar Switzerland. Kuma FIFA ta saka wa’adin 19 ga Satumba ga kowace hukuma ta amshi tayin.
A nasa ɓangaren, Arsene Wenger ya jaddada cewa aikinsa a FIFA ya ƙunshi “saka ido kan nazarin bayanan ƙwallo, cibiyar horarwar FIFA ta intanet, haɓaka ilimin matasa a makarantun ƙwallo 60 da ke ƙasashe 60, da kuma gasannin ƙwallo na matasa a faɗin duniya”.















