Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 ta bai wa Afirka ƙarin dama. Amma wasu daga cikin manyan tawagogi a nahiyar suna kallon gasar daga gida.
Gasar Kofin Duniya ta bana na gudana ba tare da Nijeriya, Kamaru, Burkina Faso, Mali, da Zambia ba.
Ko rashin wasu daga cikin waɗannan manyan ƙasashe a fannin ƙwallo afa na ba ku haushi?
Da farko, tawagar Nijeriya ta Super Eagles tawaga ce mai baiwa, jan hankali, da tarin magoya baya da za su iya cika kowace sitadiyam.
Amma sun kasa shiga gasar yanzu sau biyu a jere kenan, saboda ba su halarci gasar Qatar a 2022 ba.
Ga ƙasar irin Nijeriya, wadda ke alfahari da ƙwallon ƙafa, wannan rauni ne na ƙasa. Haziƙan 'yan wasa kamar Victor Osimhen da Ademola Lookman, ba su bayyana a matakin duniya ba. Sun rasa gurbin gasar duniya a hannun Congo (DRC) a wasan share-fage na CAF.
Wasu suna cewa rashin Nijeriya babban rashi ne ga sunan Afirka a Gasar Duniya. Nijeriya na da kambin zakarun AFCON har uku, kuma suna matsayi na 25 a duniya, kuma na 3 a Afirka.
Ba su da damar yin kururuwa
Wata babbar ƙasa ita ce Kamaru, tawagar Indomitable Lions. Sun ci Kofin AFCON sau biyar, amma a wasannin cancantar gsar Kofin Duniya, sun ƙare a matsayi na biyu a rukuninsu, a ƙasan Cabo Verde, waɗanda yanzu suka fara baje kolin su a Gasar Duniya.
Kamaru na matsayi na 44 a duniya, da matsayi na 7 a Afirka, amma zakunan ba su da damar yin kurari a matakin duniya. Yanzu sun zama ‘yan kallo kawai.
Sannan akwai Zambia, ƙasar da ta lashe AFCON na 2012. An yi tsammani babba kansu, amma tawagar ta Chipolopolo sun faɗi cikin sauri, inda a wasannin cancanta suka ƙare bayan Maroko a rukuninsu na . Yanzu suna kallon Kofin Duniya ta 2026 daga kan kujera.
Burkina Faso ma ba ta halarta gasar ba. Tawagar Stallions ta zo ta biyu a gasar AFCON ta 2013, kuma ta uku a 2017, saboda ƙarfi da juriya.
Sun kai har matakin ƙarshe a wasannin cancantar Kofin Duniya na 2026, da maki 21 da nasarori 8. Wasa guda suka rasa kacal.
Amma sun gaza shiga gasar saboda lissafi. CAF na ɗaukar zaratan tawagogi huɗu ne kawai daga waɗanda suka zo na biyu a rukuninsu don su buga wasannin share-fage. Burkina Faso ba ta samu wannan damar ba.
Maƙwabtansu, Mali, su ma sun ƙare a matsayi na uku a rukuninsu na wasannin cancanta, a bayan Ghana da Madagascar. Tawagar “The Eagles” ta zo ta biyu a AFCON 1972, kuma tana cikin manyan tawagogin Afirka. Amma a yanzu ba sa gasar Kofin Duniya.
Duk da rashin waɗannan manyan ƙasashe, masana suna cewa yadda Afirka ke taka rawa a gasar Kofin Duniya zuwa yanzu abin na birgewa.
Ƙasashen Afirka ta Kudu, Masar, Ivory Coast, Tunisia, Aljeriya, Ghana, Cabo Verde, Maroko, Senegal, da Congo DR suna wakiltar nahiyar.









.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)
