| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Afirka ta Kudu na bincike kan satar makaman soji
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar dokokin Afirka ta Kudu ya yi gargaɗi, yana mai cewa lamarin ya nuna mummunan ƙamari na matsalar laifuka na ƙasar.
Afirka ta Kudu na bincike kan satar makaman soji
An fara sauraran wata ƙara ta laifi, yayin da ake bincike kan 'yansandan kwantar da tarzoma da hukumar aikin 'yansandan Afirka ta Kudu. / Reuters

Kutsen da aka yi a wani wuri na dakarun tsaron Afirka ta Kudu a Thaba Tshwane, Pretoria, ya janyo tashin hankali bayan an sace makamai, ciki har da bindigogi da rokar harba bamabamai, a lamarin da jami’ai suka bayyana a matsayin babban koma-baya ga tsaron ƙasar.

Fashin, wanda aka gano a ƙarshen watan Afrilu, amma aka ba da rahotonsa kwanan nan, inda wasu da ake zargi suka tsallaka katanga suka shiga wurin adana makamai, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar SABC ta ruwaito ranar Litinin.

An soma shari’ar laifi kan batun, inda aka fara bincike da ya haɗa da ‘yansandan kwantar da tarzoma da kuma rundunar ‘yansandan Afirka ta Kudu.

Shugaban kwamitin tsaro na majalisar dokokin ƙasar, Dakota Legoete, ya yi gargaɗi mai ƙarfi, yana mai cewa lamarin na nuna ƙamari ne na laifuka a ƙasar.

“Wannan bai shafi laifi kawai ba—yana da alaƙa da ta’addanci da kuma barazana kai-tsaye ga tsaron ƙasarmu ,” a cewar Legoete.

“Muna magana ne kan manyan makamai da za su iya tayar da manyan rukunin shaguna da lalata gidaje da kuma ruruta rikici, a yanzu su [makamakan] na hannun masu aikata laifuka. Ƙasar ba a tsare take ba.”

Tarihin laifuka

Lamarin na zuwa ne yayin da Afirka ta Kudu ke fama da yawan laifuka. Alƙaluman laifuka na rundunar ‘yansandan Afirka ta Kudu, SAPS, sun nuna cewa an yi kisan kai fiye da 27,000 daga shekarar 2023 zuwa 2024 —wato kusan ko wace rana ana aikata kisan kai 76 ne a ƙasar.

Alƙaluman na ‘yansandan sun kuma nuna cewa bindigogi aka fi aiki da su wajen aikata laifuka.

A farkon shekarar 2025, an yi amfani da bindigogi wajen kusan rabin kisan kai 5,727 da aka yi a cikin watanni uku kawai.

A cikin wannan yanayin, Legoete ya ce satar makamai na matakin soji ya ƙara hatsari ga tsaron al’umma.

“Ba mu san abin da suke shiryawa ba, kuma wannan shi ya sa wannan abun ya ƙara kasancewa mai hatsari,” in ji shi.

“Wannan ba shi ne karon farko da muka kasance a [irin wannan hali] ba .”

Ya yi ishara ga abin da ya faru a shekarar 2018 inda aka yi amfani da makaman sojin da aka sace wajen fashi kan takardun kudin da ake tafiya da su, yana mai gargaɗin cewa maimaita irin wannan matsalar na nuni ga gazawar tsari.