An ba da umarni ga dubban mazauna yankin su bar gidajensu a jihar Washinton ta Amurka a yankin Pacific na arewa maso yammaci, yayin da gobarar daji mai bazuwa da sauri da taimakon yanayin da ake ciki ya ci gaba da bazuwa ranar Asabar, inda yake barazana ga dubban gine-gine, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Gobarar ta ƙona kusan eka 3,000 na daji (kadada 1,214 ) kuma tana barazana ga kimanin gine-gine 4,000, in ji babban jami’in kula da gandun dajin jihar George Geissler, kamar yadda CNN ta ruwaito.
Jami’ai sun ce kawo yanzu ba a gane iya ta’adin da gobarar ta yi ba, amma wutar ta riga ta shafi gine-gine.
An ba da umarni mafi ƙololuwa na matakin 3 ga wasu yankuna a ƙaramar hukumar Spokane, inda jami’an ko-ta-kwana ke kira ga mazauna su “tafi yanzu domin yanayi mai barazana ga rayuwa."
An buɗe wata mafaka a wata makaranta ta yankin.
‘Za mu kasance cikin firgici’
Gwamna Bob Ferguson ya ayyana dokar ta-ɓaci a faɗin jihar da haramta kone abubuwa yayin da Hukumar Hasashen Yanayi ta ƙasar ta ba da gargaɗi na farko na mataki mai hatsarin jar tuta da ta fara bayarwa ga yankin tsakiya da na gabashin Washington.
Gwamnan ya ce Spokane na "shiga wani yanayi na rikici cikin sauri."
"Zuƙatanmu suna tare da ‘yan Washington da ke rasa gidajensu waɗanda kuma ana kuɓutar da su," kamar yadda CNN ta ambato Ferguson yana cewa.
Manjo Janar Gent Welsh na Rundunar Ko-Ta-Kwana ta Amurka ya yi gargaɗin cewa gundumomi za su iya fuskantar lalacewar ababuwa da dama.
"A lokacin da rana ta fadi, kuma rana ta fito da safe, Ina ganin za mu kasance cikin firgici idan muka ga wasu abubuwna da za su bayyana a can," in ji shi.
A fadin Washington, fiye da eka 200,000 suna ci da wuta a gobara da yawa a wurare 12, yayin da aka tura fiye da jami’an kwana-kwana 4,000, in ji jami’an jihar.
Gobarar ta kuma janyo kuɓutar da mutane daga asibitin tsaffin sojoji na Spokane da wani wurin tsaftace ruwa da kuma wurin mayar da shara makamashi.
Hukumomi sun ce iska mai ƙarfi da ba sab ganin irinsa ba a tarihi da ƙarancin ruwa cikin iska da kuma farin da ake fama da shi sun taka rawa wajen saurin griman gobara.
Kawo yanzu ana gudanar da bincike game da abin da ya haddasa gobarar ranar Asabar da rana.

















