An kashe aƙalla mutum 12 a wani sabon harin da ‘yan Boko Haram suka kai ƙauyen Nzangula da ke Ƙaramar Hukumar Gombi ta jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Harin ya faru ne da safiyar ranar Litinin, ƙasa da makonni biyu bayan da aka kashe fiye da mutane 10 a wani hari na daban da aka kai a Ƙaramar Hukumar Hong ta jihar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Wani mazaunin kauyen ya shaida wa manema labarai cewa, wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun mamaye ƙauyen, inda suka buɗe wuta kan mutane tare da ƙona gidaje.
Mutumin ya ce an gano gawarwakin mutane 11, yayin da ake ci gaba da neman ɗaruruwan mutanen da ba a san inda suka shiga ba.
Ya ce jami’an tsaro da tawagar masu aikin ceto na bincike a dazukan da ke yankin domin gano waɗanda suka ɓace.
Kazalika wani mazaunin yankin ya ce matarsa da wasu ’yan’uwansa biyu na daga cikin waɗanda aka kashe.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombi, Markus Ishaya, ya tabbatar da harin, yana mai cewa mutane 12 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata.
Ya ce ana jinyar waɗanda suka jikkata a Asibitin Cottage da ke Gombi.
Ishaya ya ƙara da cewa an sace wata mata a yayin harin, kana an ƙona cocin EYN da gidaje uku sannan an lalata shaguna biyu.
Zuwa lokacin rubuta wannan labarin, rundunar ’yansandan jihar Adamawa ba ta fitar da sanarwa kan harin ba.
















