Shugaba Erdogan ya girmama nasarar 'Canakkale' a yaƙin duniya na ɗaya
"Canakkale wani babban al'amari ne na musamman wanda bai’ tsaya ga iya yaƙi kawai ba, yanayi ne na imani da sadaukarwa, soyayya da kishin ƙasa da kuma ruhin ƙasa ga duniya baƙi ɗaya,’’ a cewar shugaba Erdogan.
A ranar Laraba shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi bikin tunawa da nasarar Canakkale a lokacin yakin shahidai ‘Gelibolu’ na Daular Usmaniyya a yakin duniya na daya.
"Canakkale wani babban al'amari ne na musamman wanda ba’ tsaya ga iya yaƙi kawai ba, yanayi ne na imani da sadaukarwa, soyayya da kishin ƙasa da kuma ruhin ƙasa ga duniya baƙi ɗaya,’’ a cewar sakon Shugaba Recep Tayyip Erdogan ga bikin cika shekaru 111 na ranar shahidai 18 ga Maris da kuma Nasarar yakin Sojojin Ruwa na Canakkale.
A cikin wani sako da Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta fitar, shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce bikin tunawa da ranar yana cike da alfahari da kuma ƙwarin gwiwa.
Yayin da ya yi tuni kan sadaukarwa da jinjina da kuma girmamawa, " ba za a taba mantawa da jaruman da suka sadaukar a Canakkale ba," in ji Erdogan: "Gwagwarmayar da aka yi a Canakkale da zuƙatan da ke cike da imani ta zama wani muhimmin lokaci na tarihi kuma alama ce da ke nuna cewa ƙasarmu ba za ta taba yin watsi da 'yancinta da cin gashin kanta ba."
A yayin da aka yi tuni da yadda "jarumai daga kowane lungu na yankin Anatolia" suka yi gaggauta yin gaba don kare ƙasarsu, kuma ƙasar - maza da mata, matasa da manya - "sun zama tsintsiya ɗaya wajen kare ƙasarsu da rayukansu," Erdogan ya ƙara da cewa:
"Irin wannan gagarumar juriya da kakanninmu suka nuna ba wai kawai ya canza makomar ƙasarmu ba, har ma da ta ƙasashen da aka zalunta waɗanda ke rayuwa a ƙarƙashin zalunci a duk faɗin duniya.
Jarumtar da aka nuna a Canakkale ɗaya ne daga cikin manyan alamomin 'yan'uwantaka ta ƙasarmu, haɗin kai da kuma makomar da ta shafi kowa.’’
Yaƙin Canakkale
Dubban sojoji sun mutu a ɗaya daga cikin yaƙe-yaƙe mafi muni a duniya shekaru 110 da suka gabata a Yaƙin Canakkale a Daular Usmaniyya a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya.
Yaƙin ya faru ne tsakanin 25 ga watan Afrilun 1915 da 9 ga Janairu 1916.
Birtaniya da Faransa sun so su samar wa ƙawarsu Rasha tsaro yayin da yankin Gelibolu ke zama hanyar teku wanda a lokacin ya kasance Daular Rasha.
Manufarsu ita ce su kama Istanbul, babban birnin Daular Usmaniyya.
Sojojin Turkiyya sun yi nasarar dakile wani harin jirgin ruwa, inda bangarorin biyu suka rasa rayukansu a lokacin yakin da ya shafe tsawon watanni takwas.
Bayan gaza samun nasara a yakin na ƙasa da suka fafata, sai sojojin mamayar suka janye.
Nasarar da aka samu a kan sojojin kawancen ta kara wa bangaren Turkiyya kwarin gwiwa, wanda daga baya ya ba ta nasara a yakin neman 'yancin kai na Turkiyya a tsakanin 1919 zuwa 1922, kuma daga karshe aka kafa jamhuriya a 1923 daga raguwar tsohuwar daular.