Babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani, ranar Laraba ya yi iƙirarin cewa fiye da sojojin Amurka 500 aka kashe a yaƙin da ya ɓarke ranar Asabar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Larijani ya ce “makirce-makircen sakarcin” Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu sun rinjayi Shugaban Amurka Donald Trump, yana mai zarginsa da “shigar da Amurkawa wani yaƙi mara adalci da Iran.”
“Yanzu dole ya yi lissafi — da aka kashe sojojin Amurka fiye da 500 cikin kwanaki kaɗan kacal, shin Amurka ce ya saka a gabansa — ko kuma Isra’ila,” kamar yadda ya rubuta.
Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta yi shelar mutuwar sojojin Amurka shida kacal tun ranar Asabar, huɗu daga cikinsu a Kuwait.
Larijani, wanda a baya ya yi aiki a matsayin babban mai ba da shawara ga Khamenei kuma a halin yanzu yana jagorantar majalisar ƙoli ta tsaron Iran, ya yi gargaɗi a wani saƙo da ya fitar a kaikaice cewa “labarin na ci gaba .”
“Shahadar Imam Khamenei za ta sa a ɗauki gagarumar fansa akanku. Idan Allah Ya Yarda,” in ji shi.
Kalamansa na zuwa ne yayin da yaƙi tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da zafafa.
Yaƙin ya ɓarke ne da wani harin haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran ranar Asabar, lamarin da ya janyo mutuwar jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, tare da wasu manyan kwamandojin soji da suka kama aiki bayan Isra’ila ta kashe magabatansu a yaƙin watan Yunin shekarar 2025 .
Kusan ‘yan Iran 1,050 aka kashe a cikin kwanaki huɗu na yaƙi kawo yanzu, in ji ƙiyasin gwamnati, ciki har da yara ‘yan makaranta a birnin Minab da ke kudancin Iran, lamarin da ya janyo Allah wadai daga sassa daban-daban.
An kai wa Khamenei hari ne a gidansa a birnin Tehran tare da iyalansa, ciki har da matarsa da ‘yarsa da matar ɗansa da mijin ‘yarsa da kuma jikokinsa.
Gwamnatin Iran ta lashi takobin ɗaukar fansa mai ƙarfi bisa kashe Khamenei, inda ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa a kan Isra’ila da sansanonin sojin Amurka a faɗin Gabas ta Tsakiya.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, Larijani ya ce Iran ta “shirya kanta domin yaƙi mai tsawo.”
Ya kuma yi watsi da tayin tattaunawa da Amurka da ministan harkokin wajen Oman, Badr Al Busaidi, mai shiga tsakanin a tattaunawar da ɓangarorin biyu, suka yi kafin yaƙi ya ɓarke, ya yi.


















