| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
An saki gomman mutanen da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara bayan wata shida a hannun ‘yanta'adda
An yi garkuwa da mutum 176 ne a lokacin wani harin ‘yanta’adda da aka kai garuruwan Woro da al’ummar Nuku a ranar 3 ga Fabrairu, wani hari da ya yi ajalin ɗaruruwan mutane, ya raba iyalai da muhallansu tare da lalata gidaje da abubuwan more rayuwa.
An saki gomman mutanen da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara bayan wata shida a hannun ‘yanta'adda
Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq. / Hoto: Gwamnatin Jihar Kwara / FB: Gwamnatin Jihar Kwara

An sako mutane aƙalla 176 da aka yi garkuwa da su lokacin harin ‘yanta’adda na ranar 3 ga Fabrairu a garuruwan Woro da Nuku da ke Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, tsakiyar Najeriya, abin da ya kawo ƙarshen kusan watanni shida da suka shafe ana tsare da su.

Gwamnatin Jihar Kwara ce ta sanar da hakan a ranar Laraba ta shafinta na Facebook. Ta bayyana sako su a matsayin wata babbar nasara, tare da yaba wa Shugaban ƙasar ta Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, da jami’an tsaro, da duk wanda ya bayar da gudummawa wajen wannan aiki.

“Alhamdulillah muna jinjina ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR, da jami’an tsaro, da kowane mutum da ya taka rawa a wannan babbar nasara. Muna godiya!” inji gwamnatin.

Duk da cewa har kawo yanzu hukumomi ba su bayyana cikakkun bayanai kan yadda aikin ya gudana ba, majiyoyi da dama daga al’ummar yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa jami’an tsaro, tare da goyon bayan kayan aikin soji, sun shiga cikin daji tun da safiyar ranar kafin labarin ‘yantar da mutanen ya isa ga al’ummomin.

Daily Trust ta rawaito Aliyu Umar, wani mazaunin yankin kuma mamba a tawagar tattaunawa ta al’umma ta hanyar wani mai shiga tsakani, yana cewa rahotannin da ke zuwa ga al’ummomin sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani aikin ceto. Ya ce mazauna yankin Wawa da ke kusa da wajen sun ba da rahoton cewa sun ga manyan motoci bakwai ko takwas tare da rakiyar tankokin yaƙi na Sojoji suna shiga cikin daji.

Ya ƙara da cewa bayanan da ke yawo a cikin al’ummomin sun nuna cewa an miƙa waɗanda aka yi garkuwar da su ga jami’an gwamnati. A cewarsa, mazauna yankin sun ba da rahoton ganin motocin bas, da motocin masu ɗauke da bindigogin soja da sauran motocin tsaro na nufar yankin.

“Ba mu yi magana da waɗanda abin ya shafa da kanmu ba a lokacin, amma duk abin da muke ji ya nuna cewa an miƙa su ga tawagar ceto,” in ji shi.

Sakin nasu na nuna wani babban sauyi bayan watanni na rashin tabbas wanda ya haifar da zanga-zanga, da roko, da kuma tattaunawa daga iyalan da abin ya shafa.

Wannan sabon ci-gaban ya zo ne kwanaki biyar kacal bayan da iyalai suka bayyana cewa ‘yanta’addan sun ƙi amincewa da kuɗi sama da Naira miliyan 155 da aka tara daƙyar ta hanyar gudummawar al’umma, da tari, da kuma siyar da abubuwa masu daraja.

An yi garkuwa da mutum 176 ne a lokacin wani harin ‘yanta’adda da aka kai garuruwan Woro da al’ummar Nuku a ranar 3 ga Fabrairu, wani hari da ya yi ajalin ɗaruruwan mutane, ya raba iyalai da dama da muhallansu tare da lalata gidaje da ababen more rayuwa na jama’a.

Kisan ya haifar da bacin rai a fadin kasar kuma ya sa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin kara tura dakarun soji da kuma karfafa ayyukan tsaro a Kaiama da yankunan da ke kusa.

Rumbun Labarai
Majalisar Wakilan Nijeriya ta aika da ƙudirin kafa ’yansandan jihohi ga majalisun dokokin jihohi
Rikicin Amurka da Iran: NLC ta nemi gwamnatin Nijeriya ta ɗauki mataki bayan litar mai ta kai N1,500
Dakarun Nijeriya sun kubutar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi
Rundunar sojin Nijeriya 'ta kashe ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP fiye da 1000 a shekara ɗaya'
Samun ɗa namiji magaji ba ya gabana - Aliko Dangote
Rundunar 'yansandan Nijeriya ta yi gargaɗi game da yiwuwar kai hare-hare makarantu da wuraren ibada
Ana zargin ‘yanta’adda da kashe aƙalla mutum 13 a wasu hare-hare a Jihar Filato ta Nijeriya
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 262, sun kuma ceto 27 da aka yi garkuwa da su
An sace malamai shida da suka je taron addu’ar APC a Zamfara
Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan 'yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari
Mutum 511 sun kamu da cutar mashaƙo a Jihar Yobe a Nijeriya
Amurka ta aika sabbin kayayyakin soji Nijeriya
Zaben Nijeriya na 2027: Matakan Tinubu na rage talauci da alƙawarin Atiku na mayar da tallafin fetur
Jakadan Nijeriya ya ziyarci ’yan kasar 198 da ke gidan yari a Indiya
Mutane da dama sun mutu yayin da wasu ke asibiti bayan sun sha wani maganin gargajiya a jihar Ondo
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kama wasu mutane da kudade da ake zargin kuɗin fansa ne
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano