Ana sa ran kasuwanci tsakanin Turkiyya da Nijeriya ya kai dala biliyan 10 saboda sabbin yarjeniyoyi

Manyan 'yan kasuwa sun ce ziyarar Shugaba Tinubu zuwa Turkiyya ta buɗe damarmaki a fannonin tsaro, ilimi, da masana'antu.

By
Cinikin shekara-shekara tsakanin Turkiyya da Najeriya a halin yanzu ya kai kimanin dala biliyan 2, amma kasashen biyu na da burin kaiwa dala biliyan 10 zuwa shekarar 2026. / User Upload

Dangantakar kasuwanci da zuba jari tsakanin Nijeriya da Turkiyya na kan hanyar faɗaɗa cikin sauri, bayan rattaba hannu kan fiye da yarjejeniyoyi tara a yayin ziyarar shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu a Turkiyya, in ji Dele Oye, shugaban Hukumar Kasuwancin Nijeriya da Turkiyya.

Yayin da yake magana da Anadolu, Oye ya ce yarjejeniyoyin sun shafi ilimin manyan makarantu da na gaba, tsaro, kasuwanci, tsara al'ummar ƙasa a ƙasashen waje, kayayyakin halal, da sauran muhimman sassa, duka ana ana sa ran za su sauƙaƙa kasuwanci da ayyuka ga kamfanonin Turkiyya a Nijeriya.

“Waɗannan yarjejeniyoyi za su faɗaɗa fagen aiki kuma su sauƙaƙa harkokin kamfanonin Turkiyya da ke son zuba jari da yin kasuwanci a Nijeriya,” in ji Oye.

Ya ce, Nijeriya, ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka wadda ke da fiye da mutane miliyan 230, tana ba da babbar kasuwa ta masu amfani da kaya, kuma dandali ne mai muhimmanci don samun damar shiga kasuwannin nahiyar.

“Nijeriya na ba da babbar kasuwa da kuma ƙofa zuwa Afirka,” in ji Oye, yana nuni da kasancewar kasar mamba a Shirin Yarjejeniyar 'Yancin Kasuwanci ta Nahiyar Afirka (AfCFTA), wadda ke ba da damar shiga kasuwar fifiko mai mutane biliyan 1.3.

Ya kuma ambata hulɗar kasuwanci ta musamman da China ta kulla da ƙasashe 53 na Afirka a 2025, yana cewa kamfanonin Turkiyya da ke aiki a Nijeriya za su iya amfani da ƙasar a matsayin gada don cinikayya da China.

“Saboda haka, babbar dama ce ga kamfanonin Turkiyya su kafa aiki a Nijeriya, su yi amfani da Nijeriya a matsayin ƙofa don shiga kasuwannin Afirka,” in ji shi.

Tallafin Turkiyya ga tsaron Nijeriya

Hulɗar tsaro ta kasance wani muhimmi ginshiƙi na dangantakar. Oye ya yi godiya ga Turkiyya kan goyon bayanta wajen magance matsalolin tsaro na Nijeriya, yana mai cewa ministan tsaron Nijeriya da manyan hafsoshin soji suna cikin tawagar shugaban ƙasa.

“A halin yanzu, Turkiyya na samar da jiragen sama, helikofta da kuma manyan kayayyakin masana'antu da dama zuwa Nijeriya. Mun zo nan ne don gina wannan haɗin-gwiwa domin mu ƙara faɗaɗa kasuwanci,” in ji shi.

Oye ya ce ƙasashen biyu sun kafa Kwamitin Haɗin-Gwiwa Mai Ƙarfi kan Tattalin Arziƙi da Kasuwanci, wanda ke nufin rage haɗarin zuba jari da inganta damar shiga kasuwa.

Burin dala biliyan 10

Adadin ciniki na shekara-shekara tsakanin ƙasashen ya kai dala biliyan 2 a halin yanzu, amma zai iya wuce dala biliyan 10 nan da 2026, in ji shi, yana danganta hakan ga tasirin sabbin yarjejeniyoyin suka samar.

“Babu gida a Nijeriya da ba shi da kaya samfurin Turkiyya,” in ji Oye, yana bayyana hangen nesa na ƙarin zurfafan hulɗar tattalin arziƙi da cewa “mai kyau ce, mai kyau ce, mai kyau ce.”

Ya ƙara da cewa gyare-gyaren tattalin arziƙin Nijeriya da ake aiwatarwa suna fara nuna sakamako, inda aka samu ribar ciniki a cikin shekaru biyu da suka gabata da kuma dakatar da matsalar giɓin ciniki na dindindin.

Banda tattalin arziƙi, Oye ya ce dangantaka tsakanin Nijeriya da Turkiyya tana ƙarfi a fannonin siyasa, al'adu, da diflomasiyya, abin da ya samu ƙarfin-gwiwa daga rashin kasancewar tarihin mulkin mallaka tsakanin ƙasashen biyu.

“A gare mu a Nijeriya, za a iya ɗaukar Turkiyya a matsayin gida na biyu. Haka kuma, Nijeriya na iya zama gida na biyu ga kamfanonin Turkiyya,” in ji shi, yana neman kamfanoni su amfana daga abin da ya kira hanyar maraba ta musamman daga gwamnatocin biyu.