| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Shugaba Erdogan ya taya tawagar Sultans of Net ta Turkiyya murnar lashe gasar ƙwallon raga ta mata
Tawagar ƙawallon raga ta mata ta Turkiyya ta doke Brazil da ci 3-1 a wasan ƙarshe na gasar FIVB ta 2026, inda ta lashe gasar a karo na biyu bayan kafa tarihi a shekarar 2022.
Shugaba Erdogan ya taya tawagar Sultans of Net ta Turkiyya murnar lashe gasar ƙwallon raga ta mata
Wannan shi ne karo na biyu da tawagar Turkiyya ta lashe gasar kwallon raga ta kasa a tarihin gasar wanda aka soma a 2018 / TRT Afrika Hausa

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya taya tawagar ƙwallon raga ta mata ta ƙasar murna bayan ta doke Brazil a wasan ƙarshe na gasar ƙwallon raga ta FIVB ta 2026.

"Ina taya murna ga ƙungiyar ƙwallon raga ta mata ta ƙasa, wadda ta sa dukkan 'yan ƙasar Turkiyya alfahari, inda ta doke Brazil a wasan ƙarshe na gasar Nations League da kuma zama zakara," kamar yadda Shugaba Erdogan ya wallafa a shafinsa na NSosyal a ranar Lahadi.

A wani ɓangare kuma, shugaban ya taya duk wanda ya ba da gudunmawa ga nasarar ƙungiyar ta ƙasa, musamman 'yanwasa da ma'aikatan horaswa ta ƙungiyar murna ta wani kira ta wayar tarho.

Tawagar ƙawallon raga ta mata ta Turkiyya ta doke Brazil da ci 3-1 a wasan ƙarshe na gasar FIVB ta 2026, inda ta lashe gasar a karo na biyu bayan kafa tarihi a shekarar 2022.

An buga wasan ƙarshen ne a filin wasa na East Asian Games Dome da ke yankin Gudanarwa ta Musamman na Macau da ke ƙasar China, inda Turkiyya ta fafata da tawagar Brazil da ke zama ta 2 a gasar ta duniya.

Kazalika ƙungiyar ta Turkkiyya ta lashe gasar ne bayan sake kai wa matakin karshe a jere sau takwasa tun soma gasar a shekarar 2018.

Tawagar Sultans of the Net, kamar yadda aka fi sani da su, sun taka rawar gani wajen doke China a wasan kusa da na karshe don lashe gasar gaba ɗaya.

A shekarar 2023 ne tawagar ta lashe gasar bayan da ta doke China a wasan karshe, haka kuma ta zo ta biyu a 2018 inda Amurka ta lashe gasar wasan.

A yayin da ta sake kai wa zuwa karshen wasan bayan shekaru uku, Turkiyya ta kara yawan lambobin yabo a gasar zuwa hudu, inda ta samu zinari sau biyu da azurfa ɗaya da kuma tagulla ɗaya, wanda hakan ya sanya ta zama daya daga cikin kungiyoyin da suka fi samun nasara a gasar.

Kocin ƙungiyar ta ƙasa Daniele Santarelli na ci gaba da nuna bajintarsa ga samun nasarar Turkiyya a gasar.

Kocin wanda ɗan asalin ƙasar Italiya ne, ya karbi ragamar horaswa na ƙungiyar a shekarar 2023, inda ya lashe lambar zinare sau uku tare da tawagar kasar.

Bayan jagorantar Turkiyya zuwa lashe gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasa ta mata a shekarar 2023, Santarelli ya kuma jagoranci tawagar zuwa gasar ta 2026. Haka kuma ya jagoranci ƙungiyar zuwa lashe gasar cin kofin Turai ta 2023.

Santarelli ya kuma lashe lambar azurfa tare da Turkiyya a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIVB ta 2025, inda jimillar lambobin yabo da ya samu tare da ƙungiyar ta ƙasa ya kai zuwa huɗu.

Turkiyya ta rama kashin da ta sha a hannun Brazil a wasan lashe tagulla a gasar Olympics ta Paris ta 2024.

Bayan shafe shekaru biyu da shan kaye a hannun Brazil a Paris, Turkiyya ta sake kara wa da tawagar a bana inda ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ƙasa.

Ƙasar Brazil ta sha kashi a hannun Amurka a wasan ƙarshe ta 2018, da 2019 da 2021, sai kuma a 2025 inda Italiya ta doke ta kafin yanzu Turkiyya ta lallasa ta a wasan ƙarshe na 2026.