AU: Shugabannin Afirka sun ƙaddamar da taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka da batun ruwa da sauyin yanayi
Shugabannin na Afirka sun buɗe taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa na Ethiopia da batutuwan samar da ruwa, matsalolin sauyin yanayi da kuma ƙarfafa wakilcin Afirka a hukumomin duniya.
Shugabannin kasashen Afirka sun taru a Addis Ababa babban birnin Ethiopia a ranar Asabar don zama na 39 na Majalisar Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wani taron kwanaki biyu da a bana ya mayar da hankali kan samar da ruwa, matsalolin sauyin yanayi da kuma ƙarfafa wakilcin Afirka a hukumomin duniya.
Shugabannin za su ƙaddamar da taken na AU na shekarar 2026 — "Tabbatar da Samun Ruwa Mai Dorewa da Tsarin Tsabtace Muhalli Mai Aminci don Cim ma Manufofin 2063".
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da Firaiministan Italiya Giorgia Meloni da Firaiministan Falasdinu Mohammed Mustafa, da wasu shugabannin ƙasashen waje suna halartar taron a hedkwatar AU, abin da ke nuna ƙaruwar hulɗa ta duniya kan muhimman batutuwan ci gaban Afirka da na tsaro.
Bayan tattaunawa kan tsarin gudanar da ruwa da juriya ga sauyin yanayi, ana sa ran shugabannin za su duba halin zaman lafiya da tsaro a fadin nahiyar sannan su yi bitar su ci gaban manufofin 2063 — waɗanda su ne manyan burinka ƙungiyar ta AU na tsawon lokaci — sannan su yi nazari kan hanyoyin inganta tsare-tsare da da ɗorewar hanyoyin samun kuɗin ƙungiyar.