Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta samu nasarar kammala jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya domin Aikin Hajjin 2026 kafin wa’adin da aka tsara, a shirye-shiryen fara gudanar da ibadar bana.
NAHCON ta sanar da cewa jirgin ƙarshe na jigilar maniyyata ya tashi da misalin ƙarfe 10:44 na safiyar Alhamis, 21 ga Mayun 2026, wanda shi ya kawo ga nasarar kammala aikin jigilar da aka fara tun ranar 3 ga Mayu.
Jirgin na ƙarshe, wanda kamfanin Max Air ya yi aikin jigilar, ya ɗauki maniyyata daga Jihar Zamfara daga Filin Jirgin Sama na Gusau zuwa Saudiyya.
A cewar hukumar, an gudanar da jigilar jumullar jirage 98 cikin kwanaki 18, inda ake gudanar da kusan jirage biyar a kowace rana a tsawon aikin.
An bai wa Nijeriya kujerun maniyyata 50,000 domin Hajjin 2026, ciki har da kujeru 9,750 na kamfanonin jirgin yawo masu lasisi, jami’an tallafi da sauran jami’ai. NAHCON ta bayyana cewa an yi nasarar jigilar kusan maniyyata 39,000 ƙarƙashin tsarin gwamnati zuwa ƙasa mai tsarki, baya ga jami’ai da wakilan gwamnati.
Hukumar ta ce wasu kaɗan daga cikin masu niyyar zuwa Hajji sun kasa tafiya saboda wasu dalilai da ba a iya kauce musu ba kamar rashin lafiya da mutuwa bayan an ba su biza.
Hukumar NAHCON ta gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar aikin cikin tsari, lumana da kwanciyar hankali, tare da yaba wa dukkan ɓangarorin da suka ba da gudunmawa wajen gudanar da aikin.
Shugaban Hukumar kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya yaba da jajircewa da ƙoƙarin jami’an hukumar, hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, kamfanonin yawon buɗe ido, kamfanonin jiragen sama, hukumomin tsaro da kwamitocin gudanarwa.
Ya kuma yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima bisa goyon baya da kulawar da suka bayar wajen tabbatar da jin daɗi da tsaron maniyyatan Nijeriya duk da ƙalubalen siyasa da zamantakewar duniya
Yayin da maniyyatan ke ci gaba da zama a Saudiyya domin gudanar da ibadar Hajji, hukumar ta buƙace su da su kasance masu haƙuri, ladabi da bin doka a duk lokacin Aikin Hajjin.
NAHCON ta kuma shawarci maniyyata da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin Hajji da Saudiyya ta gindaya tare da ci gaba da ba jami’ai haɗin kai domin gudanar da aikin cikin nasara.
Hukumar ta tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen ayyukan Masha’ir kuma za a ci gaba da sanya ido sosai domin tabbatar da jin daɗi da walwalar maniyyatan.
A gefe guda, NAHCON ta bayyana cewa an fara shirye-shiryen dawo da maniyyata gida, inda ake sa ran fara jigilar dawowa Nijeriya daga ranar 3 ga Yunin, 2026.
Hukumar ta ƙara da cewa za a fara shirye-shiryen Hajjin 2027 nan da nan bayan kammala Hajjin bana domin ƙara inganta ayyuka da kuma ɗorawa kan nasarorin da aka samu.
A ƙarshe, NAHCON ta yi addu’ar Allah Ya karɓi Hajjin maniyyatan tare da dawo da su gida Nijeriya lafiya.


















