| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Shugaba Erdogan ya yi taron cika shekaru shida da sake bude Hagia Sophia don Ibadar Musulmai
Shuaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Hagia Sophia za ta ci gaba da amon kiran Sallah a yayin da Turkiyya take bikin cika shekaru shida da sake bude Masallacin bayan wkashe tsawon shekaru yana matsayin gidan adana kayan tarihi.
Shugaba Erdogan ya yi taron cika shekaru shida da sake bude Hagia Sophia don Ibadar Musulmai
Shugaba Erdogan ya yi taron cika shekaru shida da sake bude Hagia Sophia don Ibadar Musulmai

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Jumma'a ya yi bikin cika shekaru shida da sake bude Babban Masallacin Hagia Sophia don ibadar Musulmi.

A cikin wani rubutu da ya yi a shafin sada zumunta na NSosyal na Turkiyya, Erdogan ya ce: "Shekaru shida da suka gabata rana irin ta yau, Hagia Sophia ya dawo da asalinsa bayan shekaru 86.

“Da yardar Allah, wannan wurin ibada mai albarka zai ci gaba da yin kira zuwa ga Ibada har abada. Allah Ya albarkaci farfaɗowar Hagia Sophia."

Asali an gina Hagia Sophia a matsayin coci, kuma ya kasance wurin ibadar Kirista na tsawon shekaru 916 har zuwa lokacin da Daular Usmaniyya ta karbe iko da Istanbul a shekarar 1453, lokacin da Sultan Mehmed na II ya mayar da shi Masallaci.

Ya kasance Masallaci har zuwa shekarar 1934, lokacin da wata doka ta Majalisar Ministoci ta mayar da shi gidan adana kayan tarihi, matsayin da ya riƙe tsawon shekaru 86.

A ranar 10 ga Yuli, 2020, Majalisar Dokoki ta Turkiyya ta soke dokar 1934, inda ta share fagen sake bude abin tunawar a matsayin Masallaci.