| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Mutumin da ya fi kowa tsawo a Ghana Awuche ya rasu
Sulemana Abdul Samed, wanda ake ganin shi ne namijin da ya fi kowa tsawo a Ghana, ya rasu yana da shekara 32, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar(GBC), ta ruwaito ranar Litinin.
Mutumin da ya fi kowa tsawo a Ghana Awuche ya rasu
Sulemana Abdul Samed, wanda aka fi sani da Awuche, ya kasnace wnada ake yi wa kallon wanda ya fi ko wane namiji tsawo a Ghana.

Sulemana Abdul Samed, wanda ake ganin ya fi ko wane namiji tsawo a ƙasar Ghana, ya mutu yana mai shekara 32, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar (GBC), ta ruwaito ranar Litinin.

Abdul Samed, wanda aka fi sani da suna Awuche, ya rasu yayin da yake karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Tamale a lardin arewacin ƙasar, kamar yadda GBC ta ruwaito.

Ba a bayyana dalilin rasuwar Awuche ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Ɗan ƙasar ta Ghanan mai tsawon ƙafa bakwai da inci huɗu ya sha fama da matsalar tafiya da kuma matsalolin lafiya saboda da yawan sinadarin girma da yake da shi a jikinsa.

An tabbatar da cewa yana da wata cuta ta ‘acromegaly’ wadda ke samuwa sakamakon yawan sinadarin girma a jiki, lamarin da ke haddasa girman hannaye da ƙafafuwa da fuska.

Rashin lafiyar ta sa ana yawan kwantar da Awuche a asibiti, lamarin da ya sa aka nemi taimakon jama’a domin biyan kuɗin maganinsa a shekarar 2022.

Awuche ya yi karatu a arewacin Ghana kuma ya yi aikin kanikanci daga bisani.