| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Majalisar dokoki ta soke umarnin kamen da kwamitinta ta yi wa Mele Kyari
Majalsair ta soke wannan ne ranar Alhamis inda ta ce Shugaban ƙasa da majalisar dokokin ƙasar ne ke iya ba da wannan umarnin.
Majalisar dokoki ta soke umarnin kamen da kwamitinta ta yi wa Mele Kyari
Mele Kyari, tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya, NNPCL / NNPCL

Majalisar dokokin Nijeriya ta soke umarnin kamen da wani kwamitin asusun gwamnati na majalisar ya bayar na kama tsohon shugaban kamfanin man Nijeriya (NNPCL)m Mele Kyari.

Majalsair ta soke wannan ne ranar Alhamis inda ta ce Shugaan ƙasa da majalisar dokokin ƙasar ne ke iya ba da wannan umarnin.

Lamarin ya auku ne bayan damuwar da shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Opeyemi Bamidele, ya nuna game da matakin da kwamitin ya ɗauka da kuma kalaman da aka ruwaito cewa Sanata Adams Oshiomhole ya furta a wani zaman bincike da aka yi kwanan nan game da kamfanin man ƙasar.

Kwamitin asusun gwamnatin na majalisar ya ba da umarnin kama tare da gabatar da Kyari a gabansa ne game da tambayoyin da ba a warware ba game da kuɗin da ya kai naira tiriliyan 210 a cikin asusun kamfanin NNPCL daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Sa dai kuma da yake jawabi a zauren majalisar, Sanata Bamidele ya ce kwamitin ya zarce ikonsa ta hanyar neman ba da umarnin kamo shugaban kamfanin ba tare da tuntunɓar shugabanƙasa ko kuma shugaban majalisar ba kamar yadda doka ta tanada..

Ya kuma nuna damuwa game da kalaman da aka jiɓinta wa Oshiomhole, wanda rahotanni suka ce ya bayyana NNPCL a matsayin “wani gungun masu aikata laifuka da ɓarayi” a lokacin ganawar kwamitin da jami’an kamfanin.

Bamidele ya ce irin waɗannan kalaman za a iya musu fassara ayyana kamfanin a matsayin mai liafi tun kafin a kammala wani bincike ko kuma wat shari’ar kotu .