An kama mutum biyar kan harbin bindiga ba bisa ƙa’ida ba da 'ya kashe' yarinya Maiduguri a Nijeriya
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Asabar 4 ga Afrilun 2026, inda wasu jami’an tsaro na sa-kai da ke yin rakiya ga wani shugaban ƙaramar hukuma suka riƙa harbi sama yayin wani bikin aure a rukunin gidajen malamai na Umaru Musa Yar’
Dakarun Operation HADIN KAI sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a harbin bindiga ba bisa ka’ida ba wanda ya yi sanadin mutuwar wata ƙaramar yarinya a yankin Ngomari, a wajen birnin Maiduguri na Jihar Bornon Nijeriya.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Asabar 4 ga Afrilun 2026, inda wasu jami’an tsaro na sa-kai da ke yin rakiya ga wani shugaban ƙaramar hukuma suka riƙa harbi sama yayin wani bikin aure a rukunin gidajen malamai na Umaru Musa Yar’Adua.
Rahotanni sun bayyana cewa harbin ya jawo aka samu suɓutar hannu inda harasashi ya kauce ya samu wata yarinya ta kuma mutu take, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin al’umma.
A wata sanarwa daga bakin Laftanar Kanar Sani Uba, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas a ranar Litinin, ta ce cikin gaggawa, dakarun Operation HADIN KAI tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force sun bi sawun waɗanda ake zargi tare da kama su.
Ta ƙara da cewa a halin yanzu waɗannan mutane suna tsare a hannun sojoji, kuma za a miƙa su ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a gaban kotu bisa tanadin doka.
Hedikwatar rundunar ta yi Allah-wadai da wannan aiki, tana mai bayyana shi a matsayin rashin ƙwarewa da kuma karya dokokin amfani da makamai.
Ta jaddada cewa ƙungiyar Civilian Joint Task Force na aiki ne kawai a matsayin masu taimako, kuma ba su da izinin yin amfani da makamai ba bisa ƙa’ida ba, musamman a cikin unguwannin jama’a.
Hukumomi sun kuma fara cikakken bincike tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Borno domin gano cikakkun bayanai kan lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta duk masu laifi.
Duk da cewa an ce zaman lafiya ya dawo a yankin, dakarun tsaro sun ƙara tsaurara matakan sa ido domin tabbatar da doka da oda.
Rundunar ta kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan yarinyar da ta rasu, tare da jaddada ƙudirinta na kare rayukan fararen-hula da tabbatar da adalci.