| Hausa
Ra'ayi
TURKIYYA
5 minti karatu
Dangantakar Turkiyya da Afirka da yaƙi da FETÖ bayan yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli da aka daƙile
Musayar bayanan sirri da ƙawancen tsaro da aka kafa domin wargaza hanyoyin sadarwa na haramtacciyar ƙungiyar FETÖ a fadin Afirka ya yi babbar illa ga ayyukan ƙungiyar na dogon lokaci a nahiyar.
Dangantakar Turkiyya da Afirka da yaƙi da FETÖ bayan yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli da aka daƙile
Tun daga yukurin juyin milkin 15 ga Yuli da bai yi nasar ba, Turkiyya take aiki da kasashen Afirka don tarwatsa miyagun ayyukan FETO. / TRT Afrika / TRT Afrika

Daga Mayada Kamal Eldeen

Sakamakon mummunan yunkurin juyin mulkin da Kungiyar Ta’addanci ta Fetullah (FETÖ) ta shirya a Turkiyya ranar 15 ga Yulin shekarar 2016, ya haifar da gagarumin sauyi a manufofin kasashen waje na Turkiyya game da Afirka.

Tun bayan wannan lamari, Turkiyya ta faɗaɗa alaƙarta da nahiyar fiye da batun kasuwanci kaɗai, inda ta ƙarfafa dangantaka ta hanyar siyasa, soji da fannin tsaro, musamman ma haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci.

Musayar bayanan sirri da ƙawancen tsaro da aka kafa domin wargaza hanyoyin sadarwa na haramtacciyar ƙungiyar FETÖ a fadin Afirka ya yi babbar illa ga ayyukan ƙungiyar na dogon lokaci a nahiyar.

Babban abin da ya haifar da wannan nasara shi ne hulɗar diflomasiyya ta kai-tsaye tsakanin shugabanni wadda Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya jagoranta da kansa.

Ta hanyar tattaunawa kai-tsaye da takwarorinsa na Afirka, Shugaba Erdoğan ya gabatar da ƙwararan shaidu da ke nuna cewa FETÖ barazana ce mai sarkakiya ba ga Turkiyya kaɗai ba, har ma ga tsaron ƙasa da makomor kowace ƙasa ta Afirka da ta shiga cikinta.

Wannan matsayi mai ƙarfi ya samu karɓuwa sosai a faɗin nahiyar. Sakamakon haka, Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) da Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) sun ayyana FETÖ a hukumance a matsayin ƙungiyar ta’addanci a shekarar 2016. Wannan mataki na bai-ɗaya ya zama shaida fili ta irin gagarumin goyon baya da haɗin kan da ƙasashen Afirka ke bai wa Turkiyya.

Tarwatsa kayayyakin more rayuwa na kungiyar

Tun da farko, ƙasashe da dama ciki har da Somaliya, Sudan, Tunisiya, da Madagascar sun hango ainihin haɗarin da sauri kuma suka ɗauki mataki nan-take. Ta hanyar rufe makarantu, ƙungiyoyi, da kamfanoni masu alaka da ƙungiyar, waɗannan gwamnatoci sun miƙa dukkan kadarorinsu kai-tsaye ga Jamhuriyar Turkiyya.

A ɗaya ɓangaren kuma, a ƙasashe irinsu Senegal da Mauritania, ƙungiyar ta’addancin ta shafe shekaru da dama tana gina kanta a cikin gudanarwar gwamnati da manyan iyalai na cikin gida, tana gudanar da ayyuka a asirce ta hanyar cibiyoyin ilimi.

Kodayake waɗannan hanyoyin sadarwa masu tushe sun haifar da gagarumin ƙalubale ga tsarin zamantakewar al’umma da kuma tsaron Turkiyya, an rushe su gaba ɗaya ta hanyar ƙoƙarin diflomasiyya na Turkiyya da matakan kariya na musamman.

Rawar da Gidauniyar Maarif ke takawa a fannin ilimi

Maimakon barin giɓi a fannin ilimi ta hanyar rufe waɗannan makarantu kawai, Turkiyya ta dauki matakin hikima ta hanyar miƙa waɗannan makarantu ga Gidauniyar Maarif ta Turkiyya (Turkish Maarif Foundation).

Wannan mataki ya sa ba a dakatar da karatun ɗaliban Afirka ba yayin da ya ɗaukaka makarantun zuwa tsari na zamani kuma wanda ya dace da tsarin karatun manhajar ƙasa a hukumance. Wannan sauyi ya zama babban ci-gaba ga al’ummomin yankin, domin an dawo da tsarin ilimi da na zamantakewa da FETÖ ta yi amfani da su a baya cikin ƙanƙanin lokaci ta hanyar Gidauniyar Maarif.

A cikin wannan yanayi, Gidauniyar Maarif ta Turkiyya ta bunƙasa wajen kula da makarantun da aka karɓe, inda ta zama amintacciyar fuskar diflomasiyyar jama’a ta Turkiyya a fannin ilimi na ƙasa da ƙasa.

Ta hanyar aiwatar da tsarin karatu da ya mayar da hankali kan kimiyya, fasaha, dabi’un bil’adama na duniya, da kuma girmama al’adun jama’a, Gidauniyar Maarif ta Turkiyya tana kawar da gurbin akidun kungiyar da dabarun yaudara.

Tana aiki cikin cikakkiyar biyayya ga dokokin cikin gida da ‘yancin kai na ƙasashen, wannan tsari na hukuma ya samu amincewar ’yan Afirka da jami’an gwamnati ta hanyar samar da ilimi mai inganci, da ƙwararrun malamai, da guraben karatu masu yawa.

Don haka, kasancewar Gidauniyar Maarif ta Turkiyya a nahiyar bai zama garkuwa ga miyagun ayyuka kaɗdai ba, har ma ya ƙara danƙon zumunci mai ɗorewa bisa girmama juna da haɗin gwiwa mai albarka ba tare da mulkin mallaka ba.

Sabanin ra’ayi na shiyya da ƙalubale

Duk da cewa babban kamfen ɗin yaki da FETÖ a Afirka ya samar da sakamako mai kyau ƙwarai da gaske, martanin bai kasance ɗaya ba ta fuskar hanzari da jajircewa a dukkan shiyyoyi.

Tsaurin matakan sun bambanta dangane da zurfin shigar ƙungiyar da kuma tsarin siyasa na ƙasashen da suke karɓar baƙuncinsu.

Daga ƙarshe, gagarumin yaƙin da ake yi da ɓoyayyun hanyoyin sadarwa na FETÖ a Afirka ya kasance kashi uku daban-daban bisa ga fahimtar ƙasashen: ƙasashen da suka fahimci barazanar kai-tsaye kuma suka ɗauki mataki tare da Turkiyya; waɗanda suka yi shakka da farko amma daga baya suka miƙa makarantun; da kuma waɗanda kungiyar ke ci gaba da ɓoyewa a bayan shigarta mai zurfi da kuma shingaye na shari’a ko na siyasa.

Duk da wasu matsaloli na shiyya-shiyya da ake fuskanta, fahimtar cewa FETÖ tana aiki a matsayin ƙungiyar laifuka da ta’addanci ta duniya tana samun karɓuwa kullum a faɗin Afirka, kuma ana ci gaba da shirin murƙushe ta da gaske.

Haɗin kan da nahiyar ta nuna bayan yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli ya kasance wani muhimmin tarihi, wanda ya ɗaukaka dangantakar Turkiyya da Afirka zuwa ga haɗin gwiwa da aka gina a kan amincewar juna da tsaro da kuma hangen nesa.

Dr. Mayada Kamal Eldeen malamar jami’a ce a fannin kimiyyar siyasa da alakar ƙasa da ƙasa a Jami’ar Tokat Gaziosmanpaşa a ƙasar Turkiyya.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta bayyana ba lallai ba ne su zama iri ɗaya da ra'ayoyi da dab’i na TRT Afrika ba.

Rumbun Labarai
Jami’an leƙen asiri na Turkiyya sun kama wani babban jami’in Daesh a Syria
Manufofi da gwamnatin Netanyahu 'nauyi' ne ga Isra'ila da yankin da tsaron duniya: Ministan Turkiyya
Emine Erdogan ta karbi bakuncin matan shugabannin NATO don tattaunawa kan yara, fasaha da tsaro
Shugaba Erdogan ya ce taron NATO a Ankara ‘nasara ce ta tarihi’
Taron Trump-Erdogan: Amurka za ta ɗage wa Turkiyya takunkumai, za a yanke hukunci kan F-35 nan kusa
Tsaron Turai ba zai ta’allaka ga Tarayyar Turai ba, in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan
Taron Koli na NATO a Ankara na nuna muhimmiyar rawar Turkiyya a harkar tsaro da diflomasiyyar duniya
Muhimmin labarin fursunonin yaki Turkawa da ya sauya fasalin aƙidun horon sojojin NATO
Turai za ta yi amfani da taron NATO a Ankara ta nuna wa Trump kyakkyawar niyyarta kan tsaro: Jamus
Shugaban Turkiyya Erdogan ya karɓi baƙuncin Firaministan Pakistan Sharif a Istanbul
Salon Turkiyya na sasanci da taimakon tsaro yana inganta harkar tsaro a Afirka
Yadda Turkiyya ke ƙarfafa rawar da take takawa a NATO kafin babban taron ƙawance a Ankara
Shugaba Erdogan ya soki Isra'ila game da gangamin ɓata suna da ƙarairayi kan Turkiyya
Tawagar majalisar dokokin NATO ta ziyarci kamfanin Baykar mai ƙera jirage marasa matuƙa a Ankara
Taron NATO na Ankara zai kasance "babban dandali mai ƙarfi na musayar ƙwarewa: Erdogan na Turkiyya
Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya na neman a bunkasa kasuwanci a tsakanin duniyar Musulunci
Ma'aikatan agajin Turkiyya sun fara aikin ceto a Venezuela bayan girgizar ƙasa
Turkiyya ta tura tawagar bincike da ceto zuwa Venezuela bayan iftila'in tagwayen girgizar kasa
Shugaban Turkiyya da na Mauritaniya sun tattauna dangantaka tsakanin ƙasashensu da batutuwan yanki
'Ankara za ta ƙara ɗaukaka a diflomasiyyar duniya ta hanyar karbar tarukan NATO da ƙasashen Turkawa'