| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Trump ya ce ba za a yi yarjejeniyar nukiliya da Saudiyya ba sai ta amince da gyara alaƙa da Isra'ila
Saudiyya ta ce ba za ta sa hannu a kan Yarjejeniyar Ibrahim ba sai an samar da ƙasar Falasdinawa mai gashin kanta.
Trump ya ce ba za a yi yarjejeniyar nukiliya da Saudiyya ba sai ta amince da gyara alaƙa da Isra'ila
Trump ya ce ba za a yi yarjejeniyar nukiliya da Saudiyya ba sai ta amince da gyara alaƙa da Isra'ila

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce amincewa da yarjejeniyar makamashin nukiliya ta farar-hula tsakanin Amurka da Saudiyya na da sharadin cewa Saudiyya ta shiga Yarjejeniyar Abraham, wadda ta shafi daidaita hulɗar diflomasiyya da Isra'ila.

Ya kuma jaddada cewa ba za a ba da izinin wadatar da uranium (uranium enrichment) ba.

Trump ya bayyana cewa Amurka da Saudiyya sun cim ma yarjejeniya kan makamashin nukiliya na farar-hula, wadda za ta bai wa Saudiyya damar gina tashoshin nukiliya ta amfani da fasahar Amurka. Sai dai ya ce shirin zai kasance ne kawai domin amfani na zaman lafiya, ba na soja ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce, "Yarjejeniyar makamashin nukiliya ta farar hula (ba za a yi wadatar da uranium ba) za a amince da ita, amma hakan gaba ɗaya ya dogara ne kan Saudiyya ta shiga Yarjejeniyar Abraham."

Ya ƙara da cewa Amurka ba ta adawa da cibiyoyin makamashin nukiliya na farar hula muddin ba sa wadatar da uranium.

Tun da farko, Saudiyya ta sha bayyana cewa ba za ta shiga Yarjejeniyar Abraham ba sai an cimma matsaya kan wata hanya da za ta kai ga kafa ƙasar Falasdinu.

Amurka ce ta jagoranci ƙulla Yarjejeniyar Abraham a wa'adin mulkin Trump na farko domin ƙarfafa alaƙa tsakanin Isra'ila da ƙasashen Larabawa. Ya zuwa yanzu, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Bahrain da Morocco sun shiga yarjejeniyar, yayin da shigar Sudan ke jiran kammalawa.

Rumbun Labarai
Ƙanwar Kim Jong-un ta ce 'wawaye' ne kawai ke tunanin Koriya ta Arewa za ta miƙa makaman nukiliyarta
Taliban na neman ƙulla dangantaka da Amurka da sharaɗin a duba illolin yaƙin Afghanistan
Wuta za ku je idan ba ku jefa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisa ba, in ji Trump ga 'yan Republican
Shekaru 25 bayan 9/11, Amurkawa na tsoron ta’addancin cikin gida fiye da barazanar hari daga waje
Turkiyya da kasashe 7 sun yaba wa Birtaniya kan hana kawo kaya daga haramtattun mazaunan Isra'ilawa
An samu sojojin Jamus da laifuka kusan 2,000 da suka shafi cin zarafi ciki har da lalata da yara
Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin kafa rundunar sojin ruwa mai amfani da makaman nukiliya
Faɗaɗa Yarjejeniyar Makka: Me Bangladesh za ta iya kawo wa ƙawancen?
Kotu a Las Vegas ta samu tsohon jagoran 'yandaba Duane 'Keffe D' Davis da laifi a kisan Tupac Shakur
Cizon sauron da suka shiga Jamus ta jirgin sama ya kashe ma'aikatan filin jirgi biyu
Tsananin zafi ya yi ajalin mutane 15,800 a Jamus a bazarar bana
Shugaban hukumar leƙen asiri ta Rasha ya tabbatar da ganawa da Shugaban CIA a Moscow
Ambaliya da zaftarewar ƙasa a Nepal sun yi ajalin gommai da ɓatar da ɗaruruwa a kusa da iyakar China
Trump ya gabatar da yarjejeniyar shekaru 30 ta haɗin gwiwar nukiliyar Saudiyya ga Majalisar Amurka
Mummunar guguwa ta katse wutar lantarki a gidaje 26,000 a kudu maso-gabashin Faransa
An kama mutane da dama bayan zanga-zangar ƙyamar Musulunci a Amurka
Fitaccen tsohon ɗanwasan Brazil Roberto Carlos ya musulunta - Rahotanni
Fafaroma ya yi kira a kawo karshen cin zarafin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a Gabar Yamma
CIA ta yi shakkar iƙirarin da Isra'ila ta yi kan shirin halaka Trump bayan taron NATO: rahoto
Za a fara shari'ar wanda ake zargi da hannu a kashe Tupac Shakur a Amurka