Shugaban Amurka Donald Trump bai yanke hukunci kan wani tayin da aka gabatar don kawo karshen yaƙin da Amurka da Isra'ila kan Iran ba, yayin wani taro na kusan awa biyu tare da masu taimaka masa a Fadar White House, in ji kafofin watsa labarai na Amurka.
Fadar White House ba ta mayar da martani nan take kan buƙatar yin tsokaci a ranar Juma'a ba.
Wani babban jami'in gwamnati ya ce taron na kusan awa biyu tare da mashawarta kan tsaron ƙasar ya ƙare.
Tun da farko, Trump ya ce zai yanke shawara ta ƙarshe kan wata yiwuwar yarjejeniya da Iran, yayin da Tehran ke jaddada cewa kowace matsaya kan kawo ƙarshen rikicin tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran za ta dogara ne kan Washington ta daina yin 'buƙatu na wuce gona da iri'.
Babban mai shiga tsakani na Iran ya faɗa a baya cewa, Tehran za ta yarda da matakan Amurka ne kawai, ba maganganu ba, bayan mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya ce an samu ci gaba kan yarjejeniya don tsawaita hutu da samar da tsarin tattaunawa kan zaman lafiya.
Majiyoyin Amurka sun shaida wa AFP cewa yarjejeniyar na jiran amincewar Trump bayan makonni da aka tsayar da tattaunawar don kawo ƙarshen rikicin da ya mamaye Gabas ta Tsakiya kuma ya girgiza tattalin arzikin duniya.
"Zan kasance a taro yanzu, a Dakin Bayanin Halin da ake ciki, don yin yanke shawara ta ƙarshe," a cewar Trump a wani dogon rubutu a kafar sada zumunta, inda ya maimaita daɗaɗɗun buƙatunsa na cewa Iran ta amince cewa ba za ta mallaki makaman nukiliya ba kuma ta buɗe mahimman hanyoyin jiragen ruwa na Mashigar Hormuz.
Ya ce Tehran za ta cire nakiyoyi daga ruwa a mashigar, Amurka za ta janye katangar teku da ta yi ga tashoshin jiragen ruwa na Iran, kuma ƙasashen biyu za su haɗa hannu wajen kwashewa da lalata uraniumna Iran da aka sarrafa, kodayake bai fayyace ko an riga an amince da waɗannan abubuwan ba ko kuwa su ne ɓangarori yarjejeniyar da ake tattaunawa a kai.
Sakon Trump ya zo ne yayin da babban jami’in diflomasiyyar Iran ya nuna cewa Amurka na jinkirta yarjejeniyar ta hanyar yadda take gudanar da tattaunawar.
Halayyar Amurka
A wata waya da ya yi da takwaransa na Oman, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi 'ya nuna cewa cim ma yarjejeniya ta ƙarshe ya danganta ne da kawo ƙarshen halayyar Amurka ta buƙatu masu yawa da sauya matsayi da rashin daidaito', in ji ma'aikatarsa a wata sanarwa.
Tun da farko, shugaban majalisar dokokin Iran, wanda ya jagoranci tawagarsa a tattaunawar zaman lafiya da Amurka a Pakistan a watan da ya gabata, ya ce Tehran ta samu nasara 'ba ta hanyar tattaunawa ba, amma ta hanyar makamai masu linzami', kuma ya nuna shakku ga alƙawuran Amurka.
"Ba ma amincewa da bayar da tabbashi ko maganganu ba; ayyukan ne kawai suke da muhimmanci. Ba za a ɗauki mataki ba kafin ɗaya bangaren ya fara aiki," Mohammad Bagher Ghalibaf ya rubuta a X.
Fatan cim ma yarjejeniya ya ƙaru a ranar Alhamis bayan jami'an Amurka sun nuna kyakkyawar fahimta game da dabarun diflomasiyya, inda Vance ya shaida wa 'yan jarida cewa "an sami ci gaba mai yawa".
Wannan kyakkyawan fata ta wata yiwuwar yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran ta taimaka wa kasuwannin hannayen jari na Asiya a ranar Juma'a, yayinda farashin mai ya dan sauka.
Kasuwannin makamashi sun yi ta motsi bisa fatan wata yarjejeniya da za ta iya sake buɗe Tashar Hormuz, amma har yanzu Iran bata ba da tabbaci ga kowace yarjejeniya ba kuma ta nuna za ta ƙi amincewa da wata yarjejeniya da Trump ya bayyana shi kaɗai.
A ranar Juma'a, gidan labaran Tasnim na Iran, yana ambaton wani tushe, ya ce rubutun bai kammala ba kuma kalmomin wata yiwuwar yarjejeniya sun 'sha wasu canje-canje a kwanakin baya'.












