Yarjejeniyar Tsaro ta Hadin Gwiwa ta Makka wadda Turkiyya, Saudiyya da Pakistan suka sanya wa hannu ta aika da "saƙon haɗin kai da zaman lafiya a duk faɗin yankin," in ji Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a ranar Juma'a.
Shariff ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake ganawa da Ministan Muhalli da Ruwa da Noma na Saudiyya Abdulrahman bin Abdulmohsen Al Fadley, a cewar wata sanarwa daga Ofishin Firaministan na Pakistan.
Turkiyya, Saudiyya da Pakistan sun sanya hannu kan yarjejeniyar a wani taron ƙasashen uku a Makka a ranar 7 ga Agusta, inda suka yi alƙawarin ƙarfafa tsaro tare, da zurfafa haɗin gwiwar tsaro da kuma inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Fadar Al-Safa.
Shariff ya ce yarjejeniyar ta "haɗa kan ƙasashen uku".
Bangladesh na duba yiwuwar shiga yarjejeniyar
Bangladesh ta ce idan mambobin uku da suka kafa yarjejeniyar suka gayyace ta ta shiga to za ta ‘amince da hakan’.
Ministan Harkokin Waje Khalilur Rahman ya shaida wa majalisar dokoki a ranar Alhamis cewa Dhaka za ta amince da gayyatar idan Turkiyya, Saudiyya da Pakistan suka nemi Bangladesh ta shiga yarjejeniya.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan, Tahir Andrabi, ya ce yarjejeniyar "tsarin kariya ne da nufin kare zaman lafiya da kuma inganta zaman lafiyar yankin."
Ya ce yarjejeniyar ta kasance a bude ga kasashen da suka amince da wajibcin hadin gwiwa da muradun tsaro na gama gari.
"Za a yi la'akari da duk wata bukata ta a hukumance yayin tattaunawa da abokan hulɗarmu a Riyadh da Ankara," in ji Andrabi, yana mai ƙarawa da cewa aiwatar da yarjejeniyar ya kasance a matakin farko.




















