| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari
“Alƙawari na ga dukkan ‘yanwasan Nijeriya shi ne ku sa Nijeriya ta yi alfahari ku kuma dawo ga wata ƙasa mai nuna godiya,” in ji sanarwar.
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari
Tinubu ya ce duk 'yanwasan da suka janyo wa ƙasar abin alfahari za su ga nuna godiya daga Nijeriya / X/DTigressNG

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa kowace ɗaya daga cikin tawagar mata ta ‘yan ƙwallon kwandon Nijeriya kyautar dala 100,000 yayin da ya bai wa kowace jami’ar tawagar kyautar dala 50,000.

A wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, Shugaban ya bayyana cewa ya ba su kyautar ne domin cika alƙawarin da ya yi musu a lokacin da suka yi nasarar lashe gasar kofin Afirka ta mata ta ƙwallon kwando a shekarar 2025.

Baya ga kuɗaɗen shugaban ya ce gwamnatinsa ta cika alƙawura na lambobin yabo na ƙasa da gidaje masu ɗakuna uku a Abuja.

“A karon farko wata gwamnatin tarayya ta cika wannan mataki na ladan wasanni gaba ɗaya a cikin shekara ɗaya,” kamar yadda Shugaba Tinubu ya bayyana a sanarwar.

“Dole muka bi tsarin da doka ta tanada wajen tabbatar da cewa an aiwatar da dukkan alƙawuran yadda ya dace. Wannan ya ɗauki lokaci, amma dole a cika alƙawarin da aka ɗauka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana kan cika lada ta kuɗi da ta saura ga tawagar Super Falcons ta ƙwallon ƙafa ta ƙasar.

“‘Yansawan tawagar Super Falcons da jami’ansu sun riga sun karɓi takardun gidajensu da takardun lambobin yabonsu na ƙasa. Kazalika an riga an cika alƙawarin gidaje da lambobin yabo na ƙasa da na yi wa ‘yanwasan Super Eagles,” in ji shi.

Ya ce duk ‘yanwasan da suka janyo wa Nijeriya daraja sun cancanci abin da ya fi tafi.

“Alƙawari na ga dukkan ‘yanwasan Nijeriya shi ne ku sa Nijeriya ta yi alfahari ku kuma dawo ga wata ƙasa mai nuna godiya,” in ji sanarwar.