Ministocin harkokin wajen Turkiyya, Masar, Indunusiya, Jordan, Pakistan, Qatar, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun yi kakkausan suka da abin da suka bayyana a matsayin "abin takaici, mai ɓata rai kuma wanda ba za a mince da shi ba" da Ministan Isra'ila Itamar Ben-Gvir ya aikata kan mutanen da suke cikin rukunin jiragen da ke kan hanyar zuwa Gaza, waɗanda ake tsare su a kurkukun Isra'ila.
A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa a ranar Lahadi, ministocin sun ce wulakancin da Ben-Gvir ya yi wa waɗannan fursunoni wani "mugun hari ne ga ɗaukakin bil’adama" kuma "ƙarara ya saɓa wa wajibain da ke kan Isra'ila ƙarƙashin dokar jinƙai ta ƙasa da ƙasa da dokokin kare haƙƙin bil'adama na ƙasa da ƙasa."
Ministocin sun kuma yi tir da abin da suka kira ayyukan tunzura jama’a da tayar da hankali da suka saba wa doka, waɗanda Ben-Gvir da wasu jami'an Isra'ila suke yi wa Falasɗinawa a yankin Falasdinu da aka mamaye.
Sun yi gargaɗin cewa irin waɗannan ayyuka masu tayar da hankali "na ƙara haifar da ƙiyayya da tsattsauran ra'ayi" kuma suna raunana ƙoƙarin cim ma zaman lafiya na adalci da din-din-din bisa ga mafita samar da ƙasashe biyu.
Sanarwar ta yi kira a ɗauki matai kan ayyukan Ben-Gvir kuma ta bukaci matakai masu ma'ana don kawo karshen sake maimaita irin wannan tsokana da keta hakkoki.
Ta jaddada buƙatar kare haƙƙin bil'adama, tabbatar da mutunci da kyautatawa ga duk waɗanda ake tsare da su, da kuma kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa a yankin Falasdinu da aka mamaye.
Wannan matakin ya biyo bayan yaɗuwar bidiyon da ya nuna alama Ben-Gvir na tafiya cikin 'masu rajin da aka kama ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ke durƙushe cikin layuka masu matuƙar cunkoso, an ɗaure hannayensu a bayansu.
Jirgin ruwan, wanda ke ɗauke da mutane 428 daga ƙasashe 44, ya tashi ranar Alhamis daga Marmaris, Turkiyya, a ƙoƙarin karya takunkumin Isra'ila a kan Gaza, wanda ya fara daga shekarar 2007.














