Majalisar Dattawan Amurka ta kada kuri'a 50-48 don amincewa da wani Kudurin Ikon Yaƙi, da ke umartar Shugaba Donald Trump ya kawo ƙarshen yaƙi da Iran, sai dai idan Majalisar ta ba da izinin ƙarin matakin soja.
An amince da wannan mataki ƙarƙashin Sashe na 5(c) na Dokar Ikon Yaƙi ta 1973 bayan ya riga ya samu amincewa a Majalisar Wakilai.
Sanatocin jam'iyyar Republican, Bill Cassidy na Louisiana, Susan Collins ta Maine, Lisa Murkowski ta Alaska da Rand Paul na Kentucky sun haɗu da 'yan Democrat wajen goyon bayan ƙudurin.
Sanatan Democrat John Fetterman na Pennsylvania ya kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da shi, yayin da Sanatocin Republican Mitch McConnell na Kentucky da Dave McCormick na Pennsylvania ba su kada kuri'a ba.
Adawa ta bangarori biyu
Babau tabbas kan tasirin aiwatar da wannan mataki a zahiri, tunda Washington da Tehran sun riga sun cim ma wata yarjejeniya ta wucin gadi ta zaman lafiya.
Duk da haka, wannan kudurin wanda ba dole ne a yi aiki da shi ba yana nuni da babbar adawar majalisun Amurka da yaƙi zuwa yanzu, bayan kuri'u tara da da aka kaɗa a baya, waɗanda ba su samu rinjayen da ake buƙata a Majalisar Dattawa ba.
Kuri'ar ta biyo bayan makonni ana yaƙin da ya dagula kasuwannin makamashi na duniya kuma suka sa farashin mai a ya tashi sosai a Amurka.
Kuri'ar Majalisar Dattawan ta zo ƙasa da mako guda bayan gwamnatin Trump ta sanar da fahimtar juna ta wucin gadi tsakaninta da Iran, da nufin dakatar da tashin hankali yayin da tattaunawa don cim ma sulhu mai faɗi ke ci gaba.
A ranar 17 ga Yuni, Trump da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimta juna a wurare daban-daban, domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Yanzu ɓangarorin biyu suna cikin zuzzurfar tattaunawa cikin lokacin tsagaita wuta na kwanaki 60, suna ƙoƙarin warware sabani kan shirin nukiliyar Iran da kuma dawo da jigilar kasuwanci ta Mashigar Hormuz zuwa matakin da yake kafin rikici.















