| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun lalata maɓoyar 'yan Boko Haram a Sambisa, sun kashe 'yan ta'adda masu yawa
A ‘yan watannin nan, mayakan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare a jihohin Borno da Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya, abin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane, cikin har da janar-janar na soja.
Sojojin Nijeriya sun lalata maɓoyar 'yan Boko Haram a Sambisa, sun kashe 'yan ta'adda masu yawa
Wannan mataki ya matukar raunana karfin Boko Haram a yankin, a cewar rundunar sojin kasar. / AP / Reuters

A wani gagarumin samame na haɗin gwiwa da sojojin sama da na ƙasa suka ƙaddamar a shiyyar Arewa Maso Gabashin Nijeriya, dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun yi nasarar ruguza sansanonin 'yan ta'adda tare da tarwatsa ayyukansu a yankunan Sambisa da Tumbuns, kamar yadda rundunonin sojin sama da na ƙasa suka wallafa a shafukansu na X ranar Asabar.

Farmakin, wanda aka gudanar ƙarkashin Shirin Operation DESERT SANITY V, ya kai ga kashe mayaƙan Boko Haram da dama da lalata wuraren ajiyar kayayyakinsu.

Samamen ya fara ne da luguden wuta daga jiragen yaƙin rundunar sojin saman Najeriya a ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu, 2026. Jiragen sun kai farmaki a yankin Alafa da ke cikin dajin Sambisa, inda suka ruguza wurare da matsugunan da 'yan ta'addan ke amfani da su wajen adana makamai da kayan masarufi, a cewar sanarwar da Air Kwamado Ehimen Ejodame, Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Saman Nijeriya ya fitar da tsakar daren Asabar.

Wannan mataki ya matukar raunana ƙarfin Boko Haram a yankin, a cewarsa.

A ranar Juma’a kuma, “sojojin saman sun sake kai wani harin ba-zata a yankin Metele da ke Tumbuns. Bayan bayanan sirri sun tabbatar da kasancewar 'yan ta'adda a ɓoye a wani tsibiri mai sarƙaƙiya,” a cewar Ejodame.

Arangama gaba-da-gaba

Ya ƙara da cewa, jiragen yakin sun yi ruwan bama-bamai da suka tumɓuke sansanin baki ɗaya, tare da gano cewa an kashe adadi mai yawa na ‘yan ta’addan da ke ɓoye.

A ɓangaren dakarun ƙasa kuma, sojoji tare da hadin gwiwar dakarun sa-kai na CJTF, sun yi artabu da 'yan ta'adda a hanyar Yale zuwa Sambisa. Dakarun sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda hudu, sannan suka kwace bindiga ƙirar AK-47, da harsasai, da kuma kayan abinci da ake zargin za a kai wa sauran mambobin kungiyar da ke ɓoye, a cewar sanar da Laftanal Kanal Sani Uba, Jami’in Watsa Labarai na Rundunar Operation Haɗin Kai a Arewa Maso Gabas, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Baya ga fafatawar gaba-da-gaba, rundunar ta kuma samu wata gagarumar nasara wajen kakkaɓe masu taimaka wa 'yan ta'adda.

A garin Kanama, sojoji sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa 'yan ta'adda kayayyaki, inda aka same su da kayayyaki da bidiyoyi a wayoyinsu da ke nuna alaƙa da ƙungiyar Boko Haram.

Haka kuma, wani da ya yi da’awar ya tuba daga ayyukan Boko Haram ya miƙa wuya ga sojoji a Kukawa, inda ya bayyana cewa an kama shi ne aka tursasa masa shiga ƙungiyar.

“A halin yanzu, sojoji sun tsananta sintiri a hanyoyin Damboa, Maiduguri, Gwoza, da Goniri don toshe duk wata hanyar da 'yan ta'addan ke bi wajen samun makamai ko tserewa,” kamar yadda sanarwar ta Sani Uba ta bayyana.

Zafafa haren-haren ‘yan ta’adda

Rundunar ta ce wannan matsin lamba zai ci gaba har sai an tabbatar da cewa babu sauran wani dan ta'adda da zai iya yin barazana ga tsaron ƙasar.

A ‘yan watannin nan, mayaƙan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare a jihohin Borno da Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya, abin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane, ciki har da wasu janar-janar na soja.

Lamarin ya tayar da hankulan jama’ar ƙasar, abin da ya sa aka ringa kiraye-kirayen ɗaukar matakan da suka kamata wajen daƙile sabuwar barazanar.

Gwamnatin Nijeriya da jami’an tsaro sun ce sun ɗauki aniyar tunkarar sabon ƙalubalen, da yunƙurin maido da zaman lafiya a yankin.