Burkina Faso da Mali sun daina bai wa 'yan Amurka bizar zuwa ƙasashensu
Matakin ƙasashen na Yammacin Afirka na zuwa ne a lokacin da shugaban Amurka Trump ta ƙara yawan ƙasashen da ya taƙaita ba su damar shiga ƙasarsa waɗanda suka haɗa da ƙasashen Afirka da dama.
Burkina Faso ta mayar da martani bayan sanya ta cikin jerin ƙasashen da gwamnatin Trump ta haramta wa shiga Amurka baki ɗaya.
Burkina Faso ta yanke shawarar "ɗaukar mataki irin wanda Amurka ta ɗauka na hana biza ga 'yan ƙasar Amurka" bisa ga "ƙa'idar ramuwar gayya," in ji wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Burkina Faso ta fitar a ranar Talata.
"Gwamnatin Burkina Faso ta ci gaba da kasancewa mai aiki da ƙa’idar girmama juna, daidaiton ƙasashe da kuma ƙa'idar ramuwar gayya a cikin dangantakar ƙasa da ƙasa," in ji sanarwar, tana mai jaddada cewa ƙasar ta Yammacin Afirka "ta kasance a buɗe ga haɗin gwiwa bisa girmama muradun juna da dukkan abokan hulɗarta."
Matakin ya fara aiki
Mali da Nijar ma sun mayar da martani kan matakin takaita shiga Amurka ga ‘yan ƙasashensu.
"Dangane da ƙa'idar mayar da martani, Ma'aikatar Harkokin Waje da Haɗin Kan Ƙasashen Duniya ta sanar da al'ummar ƙasa da ƙasa cewa, nan-take, Gwamnatin Jamhuriyar Mali za ta yi amfani da sharuɗɗa da buƙatu iri ɗaya ga 'yan ƙasar Amurka kamar yadda aka sanya wa 'yan ƙasar Mali," in ji Ma'aikatar Harkokin Waje ta Mali a cikin wata sanarwa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da takunkumin taƙaita shiga ƙasar, ciki har da haramcin shiga ƙasar gaba ɗaya ga wasu ƙasashe 39, mafi yawansu na Afirka.
Matakin, wadda zai fara aiki a ranar 1 ga Janairun 2026, ya hana 'yan ƙasashen da abin ya shafa shiga Amurka.