Masu shiga tsakani a yarjejeniyar Gaza suna tattauna mataki na gaba a Masar
Ganawarsu na zuwa ne kwanaki biyu bayan tawagar manyan jami’an Hamas ta gana da babban jami’in leƙen asirin Masar domin tattauna mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutan.
Tawagogi daga ƙasashe masu shiga tsakani na Turkiyya da Masar da Qatar tare da Amurka sun gana a Alƙahira domin tattauna mataki na biyu na yarjejejniyar tsagaita wuta ta Gaza, kamar yadda kafafen watsa labaran Masar suka ruwaito.
Al-Qahera News ta ba da rahoton cewa ganarwa ta ranar Talata ta ƙunshi manyan jami’an leƙen asiri daga Masar da Turkiyya tare da Firaministan Qatar.
Tawagogin sun tattauna yin aiki da Amurka "domin tabbatar da nasarar aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta "tsakanin Isra’ila da Hamas.
Babban jami’in leƙen asirin Turkiyya, Ibrahim Kalin ya gana da manyan jami’an Qatar da Masar a Alƙahira domin tattauna ababuwan da ke faruwa a Gaza.
Kalin ya tattauna da Firaministan Qatar da kuma Ministan Harkokin Wajen Ƙasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani da kuma shugaban hukumar leƙen asirin Masar Hassan Rashad.
Kalin ya nanata cewa Turkiyya za ta ci gaba da tsayawa da Falasɗinawa da dukkan ƙarfinta.
Turkiyya da Masar da Qatar da kuma Amurka suna aiki a matsayin masu shiga tsakani da kuma ba da tabbaci (garanti) na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wadda ta fara aiki ranar 10 ga watan Oktoba bayan shekara biyu na kisan ƙare dangin Isra’ila.
Tatattaunawarsu a Alƙahira na zuwa ne kwanaki biyu bayan tawagar manyan jami’an Hamas ta gana da babban jami’in leƙen aisrin Masar Hassan Rashad, domin tattauna mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutan.
Wannan matakin na da alaƙa ne da kafa gwamnati na wucin gadi da kuma ƙaddamar da dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙasa da ƙasa a Gaza.
Ƙeta dokoki na Isra’ila
Kafar watsa labaran Al-Qahera News, ta rawaito cewa tattaunawar ta yi magana kan "shawo kan ƙalubale da kuma taƙaita keta [yarjejeniyar] domin tabbatar da cewa yarjejeniyar tsagaita wutar ta ci gaba da aiki.”
A ƙarkashin yarjejeniyar tsagaita wutan, motocin kayayyakin agaji 600 ne ya kamata su rinƙa shiga Gaza kullum.
Sai dai kuma, Isra’ila na ba da iznin shiga Gazan ne ga motocin kayayyakin agaji da ba su wuce 200 ba a kowace rana.
Isra’ila ba ta mutunta yarjejeniyar ba, inda take ƙaddamar da hare-hare kusan kullum, lamarin da ya kashe aƙalla Falasɗinawa 342 tun ranar 10 ga watan Oktoba.
"A lokacin ganawar, sun kuma amince su ci gaba da ƙarfafa hadin kai da cibiyar hadin gwiwa ta soji da farar hula (CMCC) domin kawar da dukkanin ƙalubale don tabbatar da ɗorewar yarjejeniyar tsagaita wutar da kuma hana ci-gaba da saɓa wa yarjejeniyar," kamar yadda wata majiya ta sanar da kamfanin dillancin labaran Reuters, tana mai cewa masu shiga tsakanin sun kuma tattauna daƙile yadda Isra’ila take keta yarjejeniyar tsagaita wutar.
Gawar wanda aka kama
Ita kuwa ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hamas ta miƙa gawar wani sojin isra’ila ga ƙungiyar ba da agajin gaggawa ta Red Cross (ICRC) a Gaza a ƙarƙashin wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta.
Isra’ila ta tabbatar da cewa ICRC ta karɓi gawar wani ɗan Isra’ila da aka kama daga Hamas a kudancin Gaza.
Isra’ila ta gindaya sharaɗin mayar da dukkan gawargwakin waɗanda aka kama kafin a fara tattaunawar mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar.
A kan kowace gawar wanda aka kama, Isra’ila za ta miƙa gawarwakin Falasɗinawa 15.
Isra’ila ta kashe fiye da mutum 70,000, yawancinsu mata ne da ƙananan yara tare da jikkata fiye da mutum 170,700 cikin hare-hare a Gaza tun watan Oktoban shekarar 2023.