Shugaba Erdogan ya tuna da girgizar ƙasa, ya ce ‘Turkiyya ta cika alkawarinta‘ na sake gina gidaje

Shugaban Kasar ya karrama wadanda ibtila’in na 2023 ya rutsa da su inda ya kuma bayyana yadda cikin sauri aka sake gina lardunan da suka rushe.

By
Shugaba Erdogan ya ce ba za su taba mantawa da wadanda girgizar kasar ta rutsa da su a larduna 11 na Turkiyya ba. / AA Archive

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Jumma'a ya yi bikin tunawa da waɗanda girgizar ƙasa guda biyu suka shafa a ranar 6 ga Fabrairun 2023 a kudancin Turkiyya, inda ya yi bikin cika shekaru uku da ɗaya daga cikin bala'o'i mafi muni a tarihin ƙasar, sannan ya yi alƙawarin cewa kasar ta cika alƙawarin sake gina biranen da suka lalace.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na NSosyal na Turkiyya, Erdogan ya ce Turkiyya ba za ta taɓa mantawa da waɗanda suka rasa rayukansu ba lokacin da girgizar ƙasar guda biyu suka afku a larduna 11 shekaru uku da suka gabata.

"Ba za mu manta da 'yan'uwanmu maza da mata waɗanda suka gamu da rahamar Mai Rahama saboda manyan girgizar ƙasa guda biyu da muka fuskanta shekaru uku da suka gabata a yau ba," in ji shi.

Kare ayyukan wadanda ibtila’in ya shafa

Erdogan ya jaddada cewa gwamnati ta yi alƙawarin kare kyawawan ayyukan waɗanda abin ya shafa da kuma gyara dukkan yankunan da suka lalace.

"Mun yi wa al'ummarmu alƙawarin cewa za mu ci gaba da tunawa da su a zukatanmu, mu kare abin da suka ba mu amana, mu kuma sake gina biranen da girgizar ƙasa ta lalata su," in ji Erdogan.

"A yau, da izinin Allah, mun shawo kan wannan ƙalubalen kuma mun sake ginawa tare da farfaɗo da biranenmu cikin ɗan gajeren lokaci kamar shekaru uku. Mun cika alkawarinmu," in ji shi.

Tare da sakon nasa ya yada wani bidiyo da ke nuna abubuwan da suka faru na lalacewar shekarar 2023 tare da hotunan sabbin gidaje, kayayyakin more rayuwa da wuraren hutawar jama'a da aka samar.

Girgizar ƙasa guda biyu da suka faru a tsakiyar lardin Kahramanmaras, ta kashe dubban mutane tare da haifar da barna mai yawa a kudancin Turkiyya.

Ana kuma sa ran Erdogan zai halarci bukukuwan tunawa da waɗanda abin ya shafa daga baya a ranar Juma'a.