An buɗe Taron Ilimi na Istanbul karo na biyar wanda Gidauniyar Maarif ta shirya
Wannan shekara ta gudanar da taron ya nuna manufofin nan gaba, hanyoyin masu ruwa da tsaki, da ayyuka masu kyau.
An buɗe Taron Ilimi na Istanbul na 5, wanda Gidauniyar Maarif ta Turkiyya (TMF) ta shirya don ƙarfafa tattaunawa mai zurfi kan tasirin ilimi a zamantakewa da al'adu a duniya, a ranar Juma'a.
An gudanar da taron a Cibiyar Al'adu ta Atatürk tare da Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu (AA) a matsayin abokin hulɗar sadarwa na duniya, sannan an buɗe taron tare da Uwargidan Shugaban Turkiyya, Emine Erdoğan, wacce ta kasance babbar baƙuwa a taron.
Taron, wanda zai mayar da hankali kan ci-gaban zamani da dabarun gudanarwa da kyawawan dabarun ci gaba, ya samu mahalarta da dama masu manyan muƙamai daga ƙasashe
Yayin jawabi a zaman buɗe taron, Shugaban TMF, Mahmut Özdil, ya ce gidauniyar ta ƙaddamar da wata sabuwar manhajar ilimi ta duniya a 2016 domin nuna ƙwarewar da Turkiyya take da shi a fannin ilimi ga ƙawayenta inda suke ƙara ingantata, tare da samar da “sabuwar murya” a ɓangaren ilimi.
Özdil ya ƙara da cewa cewa gidauniyar na ci gaba da aiki tare da fiye da ɗalibai 70,000 a ƙasashe 64.
"Tun daga ranar farko, burinmu bai taɓa kasancewa kawai buɗe makarantu ba," in ji shi.
"Muna tunanin gina wani tubali mai ƙarfi — wanda zai ba mu damar nazartar falsafa, manufofi da hanyoyin ilimi, da tantance ayyukanmu daidai da haka — wani muhimmin ɓangare ne na aikinmu. Wallafe-wallafenmu na ilimi, ƙoƙarin haɓaka manhajar karatu, ayyuka na dogon lokaci kamar Kundin Bayani na Turkish Maarif, da Taron Ilimi na Istanbul, wanda yanzu ya shiga bugu na biyar, su ne sakamakon da suke a bayyane na wannan ƙoƙarin.”
Ya ce taron yana bai wa manyan masana na ilimi da masu tsara manufofi na duniya damar tattauna batutuwan yau da kullum tare, yana taimakawa wajen ci gaba da sabunta hangen nesansu na ilimi — mai ƙarfi kuma kullum ana sabuntawa.
Özdil ya kuma tabo rashin daidaito a ilimi, yana jera ƙalubalen da yara marasa galihu ke fuskanta.
Taron zai ci gaba a ranar Asabar da zama na musamman.