| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'adda takwas, sun kuɓutar da mutum 125 da aka yi garkuwa da su
Sojojin Nijeriya sun kuɓutar da mutum 125 da aka yi garkuwa da su, sun kashe 'yanta'adda takwas sannan sun kama mutum 10 da ake zargi suna hada kai da 'yanta'adda a aikin da sojojin suka yi a cikin mako guda a faɗin ƙasar.
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'adda takwas, sun kuɓutar da mutum 125 da aka yi garkuwa da su
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'adda takwas sun kubutar da mutum 125 da aka yi garkuwa da su / Reuters (Wire)

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce sojin ƙasar sun kuɓutar da mutane 125 da aka yi garkuwa da su, sun kashe ’yan ta’adda takwas, tare da kama wasu mutane 10 da ake zargi da taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’adda da samar musu da kayayyakin ayyukansu, a yayin wasu ayyuka da sojojin suka yi cikin mako guda a sassan ƙasar.

A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai, Manjo Janar Michael Onoja, an gudanar da ayyukan ne tsakanin 6 zuwa 12 ga watan Nuwamba, kuma ’yan ta’adda 12 da wasu iyalansu sun miƙa wuya.

Sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya samu daga Onoja ta ce, mafi yawan mutanen da aka kuɓutar matafiya ne 119 da aka yi garkuwa da su a ranar 6 ga watan Nuwamba a kan hanyar Dutsen Kura-Bulazarma-Kamuya, da ke Buratai, ƙaramar hukumar Biu ta Jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya.

Ya ce dakarun sojin sun bi sawun maharan ne ta hanyar Mangari zuwa Dora, lamarin da ya tilasta musu barin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Mutanen da aka kuɓutar sun haɗa da maza 69, mata 35 da yara 15. Sojojin sun kuma gano wasu bama-bamai da aka ƙera a gida, waɗanda aka dasa a yankin.

Hari kan matafiya

A Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, sojoji sun kuɓutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su a yayin wasu samame daban-daban.

Haka kuma, an kuɓutar da wasu mutum uku bayan an kai hari kan matafiya a hanyar Kombo zuwa Gurusu, da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum.

Sai dai rundunar sojin ta ce direban motar da aka yi garkuwa da shi tare da sauran mutanen an gano gawarsa.

Sojojin sun kuma gudanar da wasu ayyuka a jihohi da dama, ciki har da Bauchi, Filato, Taraba, Benuwai, Nasarawa, Neja, Kwara da Oyo, inda suka kai samame wasu wuraren da ake zargin maboyar ’yan bindiga ne, suka ƙwato makamai da alburusai, tare da rusa sansanonin da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke amfani da su.

A Jihar Neja kuwa, dakarun da ke gudanar da ayyuka a gandun dajin Kainji sun tarwatsa bama-bamai guda biyar da aka ƙera a gida, sun dakile hare-hare biyu, tare da kashe wasu mutane biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne.

Sun kuma kama wasu mutanen da ake zargin suna haɗa baki da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa

Wadannan ayyukan na soji na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar wasu sassan Nijeriya, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke yin garkuwa da mutane, da kai hare-hare kan al'ummomi da kuma farmaki kan matafiya.

Garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen tsaro, musamman a yankunan arewacin ƙasar, inda manyan hanyoyi da ƙauyuka ke yawan fuskantar hare-hare.