| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dangote na shirin gina wurin ajiyar mai a Kamaru
Har wa yau wurin ajiyar man zai kare ƙasar daga ƙarancin mai kuma zai iya haɗa da bututun mai na tura tataccen mai, lamarin da zai rage kudin jigilar mai da kuma tasirin dakon mai a kan hanya.
Dangote na shirin gina wurin ajiyar mai a Kamaru
Toshon Hoto: Matatar Dangote tana samar da tacaccen mai a Nijeriya da ma ƙasashe maƙwabta

Kamfanin Dangote ya gabatar da shawarar gina wurin ajiyar mai a Kamaru yayin da yake ƙoƙarin ƙarfafa hanyoyin rarraba mai a yankin daga matatarsa mai iya tace gangar mai 650,000 a ko wace rana.

Shawarar da mataimakin shugaban kamfanin na ɓangaren mai da gas da taki, Devakumar Edwin, ya gabatar ga Firayiministan Kamaru, Joseph Dion Ngute, ranar Talata zai samar wa kamfanin wuri a tsakiyar Afirka.

Bayanai daga shawarwarin da aka wallafa a wata kafar watsa labarai ta ƙasar, Business in Cameroon, waɗanda jaridar Punch ta Nijeriya ta ambato ranar Jumma’a, sun ce wurin ajiyar da ake shirin yi zai taimaka wajen gina wurin ajiyar ko-ta-kwana ta Kamaru.

Har wa yau wurin ajiyar zai kare ƙasar daga ƙarancin mai kuma zai iya haɗa da bututun mai na tura tataccen mai, lamarin da zai rage kuɗin jigilar mai da kuma tasirin dakon mai a kan hanya.

Sai dai kuma kawo yanzu lamarin yana matakin tattaunawa ne inda ba a bayyana wata yarjejeniya ba bayan zaman. Kawo yanzu Rukunin kamfanonin Dangote bai bayyana inda za a gina wurin ajiyar ba da iya abin da zai iya ɗaukawa da ƙimar kuɗin da zai ci da kuma lokacin da aikin zai ɗauka.

Kazalika bai bayyana ko wurin zai kasance mallakar kamfanin Dangote kaɗai ne ko kuma na haɗin giwa tsakanin kamfanin da gwamnatin ƙasar Kamaru.

Idan aka samu aka gina shi, aikin zai samar da wata muhimmiyar hanyar fitar da man fetur daga matatar man Dangote a Lekki, da ke Legas, wadda aka gina domin iya biyan buƙatar mai ta cikin Nijeriya yayin da za ta samar da fetur ga ƙasashe a yankin na Afirka.

Rahotanni sun ce wurin ajiyar man da ake shirin ginawa zai bai wa kamfanin damar iya sayar da mai a Kamaru da ma ƙasashe mara teku da ke tsakiyar Afirka irin su Chadi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da suka dogara sosai kan shigowa da mai ta tashoshin jiragen ruwan Kamaru.