Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka (Pentagon) ta bayyana cewa kusan sojojin Amurka 140 ne suka jikkata a yaƙin da kasar ke yi da Iran, ciki har da sojoji takwas da suka ji raunuka masu tsanani.
“Tun farkon fara yaƙin wanda Amurka ke yi wa laƙabi da harin ‘Operation Epic Fury’, kimanin dakarun Amurka 140 ne suka ji rauni cikin kwanaki 10 na hare-haren da aka shafe ana yi ba ƙaƙƙautawa,” in ji babban kakakin Pentagon, Sean Parnell, a ranar Talata.
Parnell ya bayyana cewa sojoji takwas ɗin da suka ji munanan raunuka suna samun kulawar ƙwararrun likitoci.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters bai iya tantance nau’ukan raunukan ba, ko kuma ko suna da alaƙa da taɓin ƙwaƙwalwa (TBI), wanda galibi ke faruwa bayan an kai munanan hare-hare.
Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojin Amurka tun bayan fara rikicin a ranar 28 ga watan Fabrairu. Haka kuma ta kai hare-hare kan ofisoshin jakadanci a ƙasashen Larabawa na yankin Gulf, da otal-otal, filayen jiragen sama, sannan ta lalata wasu wuraren tatar mai.

Wadannan alkaluma sun ba da haske a karon farko kan irin asarar da sojojin Amurka suka yi biyo bayan luguden wuta da jiragen yaki marasa matuƙa na Iran, wadanda kuma suka kashe sojoji bakwai a ƙasashen Kuwait da Saudiyya.
Yayin da aka tambaye shi ko Iran ta zama abokiyar gaba mai ƙarfi fiye da yadda ya zato lokacin da Amurka ke shiryawa yaƙin, Janar Dan Caine ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa yakin bai wuce abin da suka yi tsammani ba tun farko.
“Ina ganin suna fafatawa, kuma ina yaba musu saboda hakan, amma ba na jin sun fi mu ƙarfin soja,” in ji Caine a wani taron manema labarai a Pentagon.
Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce ranar Talata za ta kasance rana mafi tsanani ta hare-haren Amurka a cikin Iran, yayin da ita kuma Iran, duk da cewa ƙarfinta ya ragu, ta lashi takobin ci gaba da fafatawa.
Munanan abubuwan da suka biyo bayan hare-haren
Mazauna birnin Tehran sun bayyana cewa babban birnin ya fuskanci wasu daga cikin munanan hare-haren sama na yaƙin, inda fashe-fashe masu ƙarfi suka girgiza unguwannin yammacin birnin, tare da rahotannin daukewar wutar lantarki a ko’ina.
Wani mazaunin yammacin Tehran ya ce yankin ya girgiza na kusan tsawon rabin sa’a yayin da hare-haren suka afku da tsakar dare.
Shi kuwa shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya yi watsi da duk wata shawara ta tsagaita wuta. Kazalika shi ma wani babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani, ya rubuta a shafinsa na X cewa “Iran ba ta tsoron barazanar cika bakin (Trump).”
A gefe guda kuma, Shugaba Trump ya bayyana a ranar Talata cewa idan har Iran ta dasa kowane irin nakiya a mashigar Hormuz, to ya kamata su cire su cikin gaggawa, inda ya ƙara da cewa yin hakan zai zama babban mataki na samun mafita.
Shugaban na Amurka ya yi gargaɗin cewa idan ba ta cire nakiyoyin nan take ba, Iran za ta fuskanci sakamakon soji irin wanda ba a taba gani ba a tarihi.















